Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da aka gurfanar da wasu marasa galihu 76 a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja a ranar Juma’a, Sanata Sani Musa (APC) dake wakiltar Jihar Neja ta Gabas ya yi alla-wadai da matakin, ya na mai fassara hakan a matsayin rashin tausayi da adalci.
Matasan su 76 da aka gurfanar sun kasance cikin waɗanda suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a watan Agusta, waɗanda aka tsare su tun lokacin.
Mai Shari’a Oboira Egwuatu shi ke hukunci game da ƙarar da aka shigar akan su inda aka gabatar da su a kotun cikin yanayi na yunwa sakamakon rashin samun isasshen abinci.
Daga nan ne aka samu wasu huɗu daga cikin su sun yanki jiki sun faɗi inda aka gaggauta fitar da su waje a ƙoƙarin kai musu ɗauki.
Sanata Musa cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana rashin jin daɗinsa game da lamarin inda ya ce duk da halin matsi da tsadar rayuwa da yaran ke fuskanta, sai da aka kai su gidan yari.
Ya kuma yi watsi da hukuncin kotun na cigaba da tsare su, ya na mai cewa hakan ya saɓa wa ƙa’idar gaskiya da adalci.
Ya yi kira ga Sufeton ƴan sanda da ya gaggauta yin bincike game da batun tare da tabbatar da yin adalci da kiyaye ƴancin matasan.
Har’ilayau, Sanatan ya ce zai cigaba da tsaya wa mazaɓarsa da dukkan al’ummar Nijeriya wajen nema musu adalci da shugabanci mai nagarta.