Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An gurfanar da shugaban ɓangaren jam’iyyar PDP, Sanata Tanimu Turaki, a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama, bisa zargin bayar da bayanan ƙarya ga ‘yan sanda.
An gurfanar da Turaki ne kan tuhuma guda ɗaya da Babban Sufeton ‘Yan Sanda (IGP) ya shigar a kansa, inda ake zarginsa da aikawa da ƙorafi a takardarsa mai ɗauke da kwanan watan 5 ga Oktoba, 2022, zuwa ga IGP, yana zargin wani mai suna Sa’idi Mohammed Mainasara da nufin cutar da shi ta hanyar amfani da ikon ‘yan sanda.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa laifin na da hukunci a ƙarƙashin sashe na 140 na dokar Penal Code.
Lokacin da aka karanta masa tuhumar, Turaki ya musanta aikata laifin, lamarin da ya sa lauyan gwamnati, Usman Rabiu, ya nemi kotu ta sanya ranar fara shari’a.
Sai dai lauyan wanda ake tuhuma, Abdulaziz Ibrahim (SAN), ya gabatar da bukatar beli ga kotu, yana mai cewa kundin tsarin mulki na shekarar 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) ya ba wanda ake tuhuma damar neman beli.
Ya kuma jaddada cewa bisa tanadin sashe na 163 na dokar gudanar da shari’o’in laifuka (ACJA), wanda ake tuhuma na da damar samun beli matuƙar babu wani dalili mai ƙarfi da zai hana hakan.
Lauyan ya ƙaryata zargin cewa Turaki ya kauce wa karɓar sammaci, yana mai cewa a lokacin da aka nemi a miƙa masa takardar tuhuma yana wajen gari ne kawai.
Domin nuna cewa zai bi shari’ar, lauyan ya ce Turaki ya halarci kotu da kansa a ranar 1 ga Afrilu, tare da neman afuwa kan rashin halartar da ya yi a ranar 26 ga Maris.
Ya roƙi kotu da ta ba shi beli bisa cancantarsa, yana mai bayyana shi a matsayin dattijo, tsohon minista, lauya mai shekaru sama da 40 a fagen aiki, kuma SAN na fiye da shekaru 20.
Sai dai lauyan gwamnati ya roƙi kotu da ta ƙi bayar da belin, yana mai cewa kotu ta yi la’akari da halayen wanda ake tuhuma kafin yanke hukunci.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Peter Kekemeke ya ce bayar da beli na cikin ikon kotu, kuma yana da alaƙa da haƙƙin ɗan adam.
Ya lura cewa duk da cewa an taɓa fitar da sammacin kama Turaki, daga baya ya bayyana a kotu kafin a aiwatar da shi, lamarin da ya sa aka janye sammaci.
Daga bisani, kotun ta yanke cewa masu gabatar da ƙara ba su gabatar da isassun hujjoji da za su hana bayar da beli ba.
Saboda haka, kotun ta bayar da belin Turaki kan kuɗi naira miliyan 100, tare da sharadin samun mutum ɗaya da zai tsaya masa da irin wannan adadi.
Kotun ta kuma ƙara da cewa dole ne wanda zai tsaya masa ya kasance ko dai SAN mai ƙwarewa na aƙalla shekaru 20 ko kuma lauya da ya kwashe sama da shekaru 40 yana aiki.
