Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Tunda aka fara cece-kuce game da kalaman shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, kan yiwuwar kawo wa Nijeriya hari, domin daƙile kisan kiyashin da ƙasar sa ke zargin Musulmi ‘yan ta’adda na yi wa mabiya addinin Kirista, hankalin jama’a da dama ya tashi, cikin wasu kuwa ya ɗuru ruwa, cacar baki tsakanin jami’an Nijeriya da na Amurka ta zafafa. Su ma kansu ‘yan ƙasa kawunan su sun rabu, tsakanin mabiya addinai mafiya rinjaye Musulmi da Kirista, kowanne ɓangare na bayyana ra’ayinsa ko dai na goyon baya, ko akasin haka.
Bayanai da ke fitowa daga wasu shugabannin al’ummar Kirista, musamman na Arewa, na nuna cewa, tun bayan hare-haren ta’addanci da aka riƙa kai wa kan majami’u da wuraren zaman Kirista, a shekaru fiye da goma da suka gabata, da kuma na baya-bayan nan da ya shafi hare-haren ’yan bindiga a jihohin tsakiyar Nijeriya, har da yankin kudancin Jihar Kaduna, ƙungiyoyin ƙasashen waje na turawa sun riƙa ganawa da shugabannin Kirista suna ɗaukar bayanai na kashe-kashen da ake yi. Kuma daga nan ne suka wallafa rahotanninsu tare da buƙatar Gwamnatin Amurka ta sa baki kan abubuwan da ke faruwa na ta’addanci da kashe-kashe akan Kirista da wurarensu na ibada. Zarge-zargen na nuni da cewa, abubuwan da ke faruwa na rashin tsaro a Arewa, an ƙirƙire su ne don cutar da Kirista da hana su ‘yancin su na yin addini, saboda ƙyamar da ake nuna musu.
Waɗannan rubuce-rubuce da rahotanni da aka riƙa wallafawa kuma aka riƙa shigar da su ga jami’ai da hukumomin ƙasar Amurka, sun ja hankalin wasu daga cikinsu har suka fara gudanar da bincike kan zargin. Rahotanni sun bayyana cewa wani tsohon jakadan Amurka Lewis Lucke shi ya fara gabatar da wannan batu a matsayin kisan kiyashi, bayan wani bincike da ya ce ya gudanar a Nijeriya, wanda kuma ya samu goyon bayan ɗan majalisar Amurka mai tsattsauran ra’ayi Sanata Ted Cruz da wasu ’yan majalisa. Za a iya cewa wannan shi ya ɗiga ɗanba a wannan dambarwar da ake ciki, wacce har ta kai ga shugaban Amurka Donald Trump ya rubuta katoɓarar da ta jawo cece-kuce tsakanin ƙasashen biyu, a shafinsa na manhajar Truth.
Sai dai abin tambaya a nan shi ne, me ya sa tun lokacin da hare-haren ta’addanci a Nijeriya ke kan ganiyar zafafa, Amurka da shugabanninta ba su yi wani abu don taimakawa Nijeriya ta shawo kan lamarin, ko kuma su yi ƙorafin da yanzu suke yi a baya ba? ‘Yan Nijeriya na ganin Amurka ta makaro da wannan barazana da take yi a yanzu, bayan da hukumomin tsaro sun fara samun galaba kan matsalar. Babu shakka akwai alamun gaskiya a zargin da wasu ke yi cewa, da walakin goro a miya.
Wasu kuma tambayar da suke yi ita ce, wanne laifi Nijeriya ta yi da har Amurka ke barazanar kai mata hari a wannan lokaci, alhalin ta kasa yin irin wannan barazanar ga ƙasar Isra’ila da take cigaba da yi wa Falasɗinawa kisan kiyashi, ko kuma a lokacin da mabiya addinin Buddha suka riƙa yi wa musulmin Rohingya kisan kiyashi. Duk babu abin da Amurka ta yi don dakatar da abin da ke faruwa, na kashe-kashe da cin zarafin ɗan adam a matsayin su na Musulmi. Amma sai ga shi akan wasu zarge-zarge marasa inganci da aka kitsa saboda son zuciya da neman haddasa fitina a arewacin Nijeriya, Trump da muƙarrabansa suna ta kumfar baki da barazanar kawo hari kan ’yan ta’adda a Nijeriya, ƙasar da take da cikakken ’yanci da zaɓaɓɓiyar gwamnati.
Wasu manazarta sun yi ta rubuce-rubuce da bayyana mabambantan ra’ayoyi dangane abubuwan da suke hasashen ya haddasa wannan barazana da cin mutunci. Ra’ayi mafi rinjaye ya karkata ne kan cewa, Amurka na jin haushin Nijeriya ne don goyon bayan da take nunawa ga Falasɗinawa, da kuma ƙin amincewar ƙasar na miƙa wani jagoran Falasɗinawa da ke Nijeriya wanda hukumomin Isra’ila suka nemi a miƙa musu shi. Sannan kuma harwayau, yankin arewacin Nijeriya na da magoya bayan gwagwarmayar Falasɗinawa da daman gaske, wanda kuma hakan barazana ce ga muradun Amurka da Isra’ila a yankin kudu da saharar yammacin Afirka. Wannan na iya zama daga dalilan da ya sa Amurka ke jin haushin Nijeriya.
Goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke cigaba da samu, da yaɗuwar manufofin ta na yaƙi da danniyar ƙasar Isra’ila, musamman a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ’yan Shi’a ta ‘yan uwa Musulmi, wata babbar barazana ce ga muradun Amurka a yankin arewacin Nijeriya da Afirka. Hakan na nuna cewa tasirin ƙasar Iran a Nijeriya na ƙalubalantar shirin Amurka na kafa sansanin sojojinta, da samun kafar haddasa rigingimu a yankin.
Kafa gwamnatin Muslim-Muslim ta shugaba Tinubu da Kashim, ta ƙona ran wasu ’yan Nijeriya da ke ciki da wajen ƙasar nan, waɗanda suke ganin ba a yi wa mabiya addinin Kirista adalci ba, yayin kafa sabuwar gwamnati. Don haka akwai yiwuwar Donald Trump da ’yan kanzaginsa na da burin haifar da fitinar da za ta tabbatar da kawar da wannan gwamnati ko ta halin ƙaƙa, domin kafa tsarin da suke so ya tafiyar da ƙasar, ba ra’ayin talakawa masu rinjaye ba.
Harwayau kuma, akwai kuma masu hasashen lamarin na da nasaba da yadda shugabannin Nijeriya suke ba da muhimmanci kan ƙarfafa hulɗar kasuwanci da ƙasar China, wacce ke daga cikin abokan adawar Amurka. Yayin da Nijeriya ta sanya hannu kan kwangiloli na miliyoyin dala kan batun da ya shafi makamashi da tsaro. Hakan yana ƙara bai wa China ƙarfin mamaye harkokin tattalin arziki a Afirka, musamman duba da tasirin da Nijeriya ke da shi a nahiyar.
Nasan ba za ku manta da yunƙurin Amurka na kafa sansanin sojojinta a Nijeriya, buƙatar da hukumomin ƙasar suka nuna rashin amincewa. Babu shakka wannan ya taɓa Amurka sosai, domin rashin sansanin su a wannan yanki na Afirka ya rage tasirinta a yammacin Afirka. Bugu da ƙari kuma ba da jimawa ba gwamnatin Amurka ta nemi amincewar Nijeriya don karɓar wasu ’yan ƙasar ɓenezuela da ta sallama daga gidajen yarin ƙasar bisa aikata laifuka daban-daban, buƙatar da shugabannin Nijeriya suka ƙi amincewa. Wannan ma ana ganin tamkar Nijeriya ta watsawa Amurka ƙasa a ido ne, don a dalilin hakan an ce dangantaka ta fara tsami a tsakanin ƙasashen biyu.
Manazarta na ganin wannan na daga cikin dalilan da ya bai wa Amurka ƙwarin gwiwa na tsoma baki cikin matsalolin tsaron Nijeriya, musamman jin irin girman zargin da ake yi wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda musulmi na yi wa Kirista kisan kiyashi. Amurka na ganin dama ta samu da za ta turo sojojinta Nijeriya su kafa sansani da sunan yaƙi da ta’addanci, don ta huce haushi kan abubuwan da Nijeriya take yi mata.
Kodayake, shugabannin Nijeriya na ƙoƙarin ganin an samu fahimtar juna da hukumomin ƙasar Amurka, don ganin ba a samu matsalar tsaro a tsakanin su ba, amma tuni wasu ‘yan Nijeriya musamman waɗanda ke ganin dacewar harin da Amurka ta ce za ta kawo wa Nijeriya suna ta murna da bayyana jin daɗinsu da hakan. Yayin da suke ganin lokaci ya yi da za a yi musu maganin ’yan ta’addan musulmi da ke samun goyon bayan sauran ’yan uwan su ’yan Arewa.
Sai dai duk da haka ba a taru an zama ɗaya ba, a yayin da wasu ke ganin ɗaukar matakin soja shi ne kawai mafita, wasu na cewa Amurka za ta iya ba da gudunmawa ga jami’an tsaron Nijeriya ta hanyar ba da tallafin makamai da bayanan sirri na yadda za a yi maganin masu ɗaukar nauyin ta’addanci da ba su tallafi, ba sai an kai ga zubar da jini ba.
Kodayake, Sakataren Ma’aikatar Yaƙi na Amurka, Pete Hegseth, ya ce tuni sun kammala tsara shirya yadda za su ƙaddamar da hare-haren su a Nijeriya, a wani tsari da suke ganin za a gudanar da shi cikin sauƙi da sauri, wasu masu nazari kan yaƙe-yaƙen da Amurka ta ƙaddamar irin waɗannan a Afghanistan da Iraƙi da ma Somaliya yaƙi ne da in an fara ba a san inda zai tsaya ba. Shugabannin Nijeriya dai na ƙoƙarin ganin Amurka ba ta kai ga fara ƙaddamar da harin soja ta hanyar keta sararin samaniyarta da ’yancinta na ƙasa mai ’yanci ba.
Bisa ga dukkan alamu dai wannan barazana da Amurka ta yi ko da ba a kai ga kai harin soja ba, Amurka ta samu nasarar ƙara sanya gaba da zargin juna a tsakanin ’yan Nijeriya, da sunan addini. Ta kuma ƙara fallasa yiwuwar samun mummunan rikicin addini a ƙasar nan, idan hukumomi ba su ɗauki matakan da suka dace ba.
Lallai ne malaman addini, musamman shugabannin Kirista, su tashi tsaye don wayar da kan mabiyansu da wanke kansu daga zargin rura wutar gaba da rikici a Nijeriya. Su tabbatar sun bayyana da haɗin kai da goyon baya ga ƙoƙarin gwamnati na samar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.
