Mabiya Shi’ah sun yi gangamin adawa da Trump

Spread the love

Yayin da aka kammala sallar Juma’a ne a jiya a masallacin Fagge da ke Jihar Kano, mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da gangamin lumana don nuna adawa da kalaman shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar kai hari ga Najeriya.

Masu gangamin sun bayyana kalaman Trump a matsayin nuna girman kai da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasar, tare da jaddada cewa Najeriya ba za ta lamunci irin wannan barazana ba.

Haka kuma an ga yadda suka riƙa ɗaga kwalaye masu ɗauke da sakonnin kira da zaman lafiya, da kuma jaddada goyon bayansu ga gaskiya, adalci, da kare ƙasar su daga duk wata barazana.

Wani daga cikin masu shirya gangamin ya bayyana cewa: “Nijeriya mallakar ’ya’yanta ce, ba ta kowace ƙasa ba. Ba za mu bari wata ƙasa ta tada mana rikici ko ta kawo mana rudani ba”, kamar yadda One News Hausa ta ruwaito.

An kammala gangamin cikin kwanciyar hankali, inda aka yi addu’o’i don neman zaman lafiya, da kariya ga Nijeriya daga dukkan wani makirci ko barazana daga ƙasashen waje.

By Babaji