Kano: Ƙaramar Hukumar Bichi ta buƙaci a samar da kasuwar dabbobi a Badume

Spread the love

Sakataren Mulki na Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, Alhaji Anas ya gabatar da wannan buƙatar samar da kasuwar dabbobi a wani gangamin taro da aka yi na samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Habaka Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano a lokacin da tawagarta ta halarci Bichi.

Sakamakon himmar gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya ƙirƙiro ma’aikatar domin jin daɗi da walwalar jama’a da kuma bunƙasa tattalin arzikinsu, Sakataren, wanda ya wakilci Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, bayan goyan baya da dimbun shawarwari ya kara da cewa, “Samun bunƙasar harkar dabbobi abu ne wanda muke maraba da shi.”

Daga bisani masu ruwa da tsakin yankin suka sake gabatar da wasu muhimman buƙatun karamar hukumar da suka hadar da; samar da kwamitin wayar da kan makiyaya baki kafin shigowarsu gari ta hanyar haɗin gwiwar manoma da makiyaya mazauna gari, daga Sashen Kula da Sulhu tsakanin Manoma da Makiyaya na Civil Defense, da kuma samar da asibitin dabbobi a Ƙaramar Hukumar daga Sashen Ma’aikatar Gona na yankin.

Saidai, jangaren jami’an tsaro, sun koka da ta’adin da ya kunno kai, inda ake shiga gonakin mutane da daddare ana kona musu amfanin gona a yankin Kyalli.

Akan haka ne suka yi kira ga al’umma tare da jan hankalin hukumomi domin daƙile matsalar tun da wuri.

Haka kuma wakilan al’umma ga gwamnati da suka zama jigon wannan taro, sun tofa albarkacinsu na abin da ya zama kiki-kaka har wa yau da kuma hanyoyin magance su bisa fahimtarsu.

“Maganar makiyaya abu biyu ne; muddin ba a fitar da labuka da mashayar ruwa ba, duk shekara haka za ai ta fama da wannan matsala”, inji Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyatti Allah a Bichi, Alhaji Tukur Abdullahi Buden Waje.

“Mu dagatai a shirye muke mu ba da dukkan wani hadin-kai wanda zai kawo mana zaman lafiya”, inji Dagacin Daddo, Malam Umar Abubakar.

Malam Sule Abdu kuwa, cewa ya yi “Tabbas an ɗauko hanyar da za a samu masalaha tsakanin manoma da makiyaya.”

Kwamishinan ma”aikatar, Dr. Aliyu Isa Aliyu Ɗan-Zabuwa, wanda Daraktan Mulki na ma’aikatar, Alhaji Yahya Sani Abbas ya wakilce shi, da ya yi alkawari tare da jaddada kudurin gwamnatin jiha karkashin wannan ma’aikata na samar da; asibitin dabbobi duk inda yakamata a fadin jihar Kano tare da samar da Mayanka a sassa daban-daban, duba da zamani domin samar da aikin yi ga wasu da habaka riba da bunkasa tattalin arziki.

A ƙarshe, ya rufe da jan hankalin alumma kada a ɗauki doka a hannu, tare da kira ga masu riƙe da sarauta cewa, “Masu sarautu don Allah a rika kula da wannan cases din na burtali, idan an samu matsala a riƙa reporting”, kamar yadda jami’ar hulɗa da jama’a ta Ƙaramar Hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta ruwaito.

By Babaji