Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta sanar da cewa ƙaramin ministan tsaron Nijeriya, Hon Bello Mohammed Matawalle zai ziyarci Jihar Zamfara ranar Alhamis mai zuwa.
Sakataren yaɗa labarai na Jam’iyyar Yusuf Idris ya ce a cikin wata sanarwa da aka bayar ga Blueprint Manhaja yau Asabar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa, da isowar sa, Matawalle zai gana da ‘yan jam’iyyar da dukkan tsoffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni da sauran shugabanni a gidansa da ke Gusau.
Matawalle zai yi taron masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar a sakatariyar Jam’iyyar APC ta jihar ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa Matawalle zai tafi garinsu Maradun don ci gaba da ganawa da ‘yan jam’iyyar da iyalansa a ranar Asabar.
Jam’iyyar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su haɗa kai sosai don gudanar da ziyarar cikin kwanciyar hankali.
“Muna kira ga ‘yan jam’iyyarmu da magoya bayanmu da su kasance masu bin doka da oda da kuma kyawawan halaye a lokacin ziyarar”.
Jam’iyyar ta gargaɗi magoya bayan jam’iyyar da kada su ɗauki wani nau’in makami na kowane iri a lokacin ziyarar.
“Mun yi gargaɗi sosai cewa babu wani makami da aka yarda a ɗauka, saboda haka a yi hattara da masu ɓata suna waɗanda za su iya hana mu samun nasarar ziyarar.
