Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar Grassroot Initiative Concept ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Mataimakinsa, Sanata Barau I. Jibrin, da cusa siyasa wajen hana tabbatar da naɗin Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaba kuma babban jami’in Hukumar kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC)
In da tace ana zargin bai wa waɗannan shugabanni na majalisar dattawa biyu cin hancin Dala miliyan 10.
To sai dai kuma, ita ma Coalition of Tinubu/Barau Support Groups ta ƙaryata zargin, tana cewa batun ƙarya ne da makirci.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Kano a ranar Juma’a, jagoran Grassroot Initiative Concept, Alwan Hassan, ya ce shisshigi daga wasu manyan ƴan majalisa ne ya jawo tsaikon tabbatar da naɗin duk da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa Ramat kuma an riga an tantance shi a kwamitin wutar lantarki na Majalisar Dattawa.
Ya bayyana Injiniya Ramat a matsayin ƙwararren masanin fasahar sadarwa da ya dace da aikin, yana mai kira ga shugabancin majalisar da su mutunta tsarin doka da kuma yanke hukunci bisa cancanta.
Sai dai a nasa ɓangaren, jagoran Coalition of Tinubu/Barau Support Groups, Kwamared Hafizu Sani Liman, ya mayar da martani yana cewa Sanata Barau ma yana goyon bayan naɗin Ramat, har ma yana tuntubar takwarorinsa domin tabbatar da shi cikin nasara.
Liman ya ce zargin da tsohuwar Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Gawuna ke yaɗawa ƙarya ce da nufin ɓata sunan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, yana mai cewa an kammala tantancewar da kwamitin wutar lantarki na majalisar ya yi, kuma ana jiran gabatar da rahoton a zauren majalisa.
Ƙungiyar ta kuma musanta zargin cewa Sanata Akpabio da Barau sun karɓi cin hanci don hana tabbatar da naɗin, tana mai cewa za su ɗauki matakin shari’a kan masu yaɗa irin wannan labari.
Dukkan ƙungiyoyin biyu sun bayyana goyon bayansu ga manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu kan dalilan da ya kawo jinkirin tabbatar da naɗin shugaban hukumar ta NERC.
