
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Matasan Arewa masu son Zaman lafiya da Ci-gaba (NYPP) ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da ya ɗauki matakin gaggawa akan zargin Sanata Shehu Umar Buba da hannu a ayyukan ta’addanci a Arewa.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kodinetanta, Kwamared Hassan Sadau, NYPP ta bayyana kaɗuwarta game da matsayin Buba Umar na cigaba da zama sanata kuma shugaban kwamitin majalisar tsaron ƙasa da leƙen asiri.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da aka ga sanatan a wani faifan bidiyo mai ta da hankali yana jagorantar zuba wasu maƙudan kuɗaɗe a wata mota a gidansa da tarin wasu babura da ƴan bindiga ke amfani da ire-irensu wajen kai farmaki a garuruwan Arewacin Nijeriya.
Lamarin da ya sa ƙungiyar take ganin hakan ka iya shafar kimar ofishinsa na shugaban kwamitin harkar tsaron ƙasa da ma majalisar baki ɗaya ganin yadda al’umma ke sa ran samun adalci daga gare shi akan lamuran tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
NYPP ta bayyana cewa, yayin da jami’an tsaro suke ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya a shiyyar da sauran sassan ƙasa, ƙulla makirci daga manyan ƙasa ka iya haifar wa hakan tsaiko da jefa sassan arewacin Nijeriya cikin hatsari mafi muni.
Ta ƙara da cewa, muddin al’umma ta cigaba da zama da tunanin Sanata Buba yana da alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci na ire-iren su Bello Turji, Adamu Aliero da Dogo Gide, hakan ka iya zama barazana ga makomar siyasar zaɓaɓɓun ƴan siyasar da ke wakiltar al’umma a matakai daban-daban na ƙasa duba da rasa rayuka da dukiyoyi da ake yi kullum a shiyyar.
Don haka ne take kira ga majalisar da ta gaggauta warware matsalolin zargin sanatan, wanda ke wakiltar yankin Bauchi ta Kudu.
