Gwamnatin Katsina za ta sakar wa ƙananan hukumomi 34 kuɗaɗensu duk wata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya yanke wannan shawara domin ƙarfafa shugabancin ƙananan hukumomi daga rushe.

Mai baiwa Gwamna Shawara kan ƙananan hukumomi da babban mai binciken kuɗin na ƙananan hukumomi Alhaji Lawal Rufa’i Safana sanar da haka lokacin da ya ke ganawa da shi da babban audita na ƙananan hukumomi da shugabannin ƙananan hukumomi da Ma’ajin su a Katsina.

Ya ce yanzu haka gwamnati na shirin biyan ƙananan hukumomin kuɗaɗen su da suka rage na watan Agusta da ya gudana.

Safana ya faɗa masu cewa dole ne a matsayin su na masu sa hannu a fitar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi dole su bi ƙa’idojin da ya shinfida kafin fitar da ko da kobo ne daga asusun ƙaramar hukuma.

Yayi gargaɗi cewa duk wanda aka samu da karya dokar to zai gamu da hukuncin mai tsanani.

Lawal Safana ya bayyana cewa a ganawar ta su, sun tattauna akan shirye shiryen kasafin kuɗi na 2026.

Ya jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na tabbatar da samar da abubuwan more rayuwa a matakin ƙananan hukumomi da zai ba al’ummar karkara more more romon dimokuraɗiyya.

By ukarofi