Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Kungiyar yaƙin neman zaɓen Mahdi Aliyu Gusau ta ƙi amincewa da ɗora sunan Bilyaminu Shinkafi a shafin yanar gizon hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, a matsayin ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a Jihar Zamfara.
Ƙungiyar ta bayyana hakan a matsayin wata dabarar da ba ta dace ba kuma ta yi alƙawarin ƙalubalantar sa a kotu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Gusau ranar Juma’a, wadda ƙungiyar yaƙin neman zaɓen ta sanya wa hannu, ta dage cewa Mahdi Gusau shine halartaccen ɗan takarar gwamna na ADC a babban zaɓen 2027 a Jihar Zamfara.
A cewar sanarwar, abun takaici da rashin aiwatar da dimokuraɗiyya ne ya sanya hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ɗora sunan wani Bilyaminu Shinkafi a shafin yanar gizon INEC a matsayin mai riƙe tuta na ADC.
Kungiyar ta kira matakin a matsayin karya dokar zaɓen da gangan, da kuma cin zarafin wakilai da ƙa’idodin dimokuraɗiyya na babbar jam’iyyar adawa ta ADC a Jihar.
Haka zalika ta bayyana fidda sunan Bilyaminu Shinkafi da INEC ta yi a matsayin yanayi mai sarƙaƙiya game da zaɓen fidda gwani na ADC wanda ya samar da Mahadi Aliyu Gusau a matsayin halartaccen ɗan takarar gwamnan.
Ta ce an gudanar da zaɓen fidda gwanin Mahadi Aliyu Gusau ne tare da jami’an INEC, hukumomin tsaro a da kuma shugabannin jam’iyya da ke kula da su.
“A lokacin zaɓen fidda gwanin, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Zamfara Mahadi Aliyu Gusau ya samu ƙuri’u 35,665 inda ya kayar da sauran ‘yan takara, kuma shugaban kwamitin zaɓe ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.”
“Munyi matukar mamakin yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar da sunan wani ba Mahadi Aliyu Gusau ba a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar a ADC.
Ƙungiyar ta bayyana matsayin ta na zuwa kotu domin dawo da ikon da aka ƙwace ma Mahadi Aliyu Gusau.
“Muna da yaƙinin cewa kotu za ta kori duk wani mai yin ƙarya ta kuma mayar wa da ɗan takarar da ya cancanta ikon, domin gaskiya tana tare da mu ba tare da wata shakka ba.” A cewar sanarwar.
