Ƙungiyar matasa a Arewa ta jinjina wa Shettima yayin murnar cikarsa shekaru 60 a duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban ƙungiyar Arewa Democratic Stakeholders Forum, Hon. Haruna Sardauna CIPAG, ya taya Maitaimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima murnar cika shekaru 60 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin mai ladabi kuma abokin tafiya na ƙwarai ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Hon. Danjuma Umoru Agaba ya fitar a ranar Laraba, ƙungiyar ta bayyana Shettima a matsayin “ɗan siyasa mai zuciyar gwal”, wanda jajircewa da ƙoƙarinsa na tallafa wa gwamnatin Shugaba Tinubu ta ke bambance shi da sauran jagororin siyasa a Nijeriya.

Ta ce, cika shekaru 60 na mataimakin shugaban ƙasar dama ce ga ‘yan Nijeriya musamman ‘yan Arewa, su taya shi murna bisa ƙwarin-gwiwa, ƙarfin ilimi da jajircewarsa kan lamuran ci-gaban ƙasa ta hanyar gudummawarsa ga tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Tinubu.

Ƙungiyar ta kuma yi masa magiya da ya mayar da hankali kan ƙalubalen da ke fuskantar matasan arewa domin tabbatar da cewa sun samu damarmakin bayar da gudummawa ga ci-gaban ƙasa domin ci-gaban arewa da ma ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, ƙungiyar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a fagen siyasar arewacin Nijeriya da su cigaba da bayar da gudummawa ga muhimman tsare-tsaren gwamnatin tarayya, tana mai cewa ayyukan ci-gaba a shiyyar suna buƙatar kama-kama daga dukkan masu ruwa da tsaki.

By Babaji

Leave a Reply