Ƙaramar hukumar Ingawa a Katsina ta kashe Naira miliyan 10 wajen samar da ruwan sha

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙaramar hukumar Ingawa ta kashe Naira miliyan 10 wajen sayen na’urar bada wutar lantarki mai amfani da hasken rana a garin Ingawa.

Shugaban ƙaramar hukumar Alhaji Labaran Magaji ya faɗa wa manema labarai haka a Ingawa.

Ya ce a baya duk wata ƙaramar hukumar na kashe Naira 200,000 wajen sayen man gas amma yanzu hakan ya zama tarihi.

Shugaban karamar hukumar wanda ya sami wakilcin daraktan mulki Mukhtar Aminu Bakori ya bayyana cewar a duk rana injin yana samar da lita na ruwa miliyan 12 zuwa yankunan.

Ya bayyana wasu aikace-aikace da gwamnatin jihar ta aiwatar da suka haɗa da gina gada a Tunas da zai haɗa garuruwan Rumawa,Danƙawa,Shabebe da wasu ƙauyuka guda 10.

Bakori ya ce gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ba ƙananan hukumomi 34 da ke jihar damar su gina asibitoci guda Uku kowanne wanda tuni ƙaramar hukumar ta kammala gina wa.

Haka kuma gwamnatin jihar ta samar da kayan aikin noman rani da suka haɗa da takin zamani da garman shanu da injiunan noman rani mai amfani da hasken rana.

Daraktan mulkin ya faɗa cewa ƙaramar hukumar ta Ingawa ta kashi fiye da Naira biliyan ɗaya wajan samadda ababe more rayuwa a sassa daban na ƙaramar hukumar.

By ukarofi