Sharhin waƙoƙin korona na Hausa na ‘Corona Blues’

Spread the love

Daga MURTALA MUHAMMED (PHD)

Sunan Littafi: Corona Blues (A bilingual Poetry Collection)

Editoci: Isma’il Bala da Khalid Imam 

Maɗaba’a: Whetstone Publishers Kano, Nigeria

ɗaukan nauyin bugawa: Gidauniyar MacArthur da Cibiyar Ilimtarwa ta ƙasa-da-ƙasa (IIE)

Adadin Shafi: 165

Lambar ɗab’i: ISBN 978-978-58335-1-5

Shekarar da aka wallafa: 2020

Sharhi: Murtala Uba Mohammed (PhD)

Shimfiɗa:

A duk lokacin da mutum ya shiga cikin damuwa da fargaba yakan nemi waraka da samun sauƙi ne ta yin amfani da hayoyin da yake ganin za su iya warware masa irin ƙuncin da ya shiga. Waƙa na ɗaya daga cikin manyan magunguna da akan yi amafani da ita don samun waraka daga cututuka. Ba wai amfanin waƙa faɗakarwa da nishaɗantarwa kawai ba, a’a waƙa wata hanya ce ta samun sasaucin rai da ɗauke damuwar daga zuciya. Waƙa kan samarwa da ma’abotanta, tun daga kan marubata da makaranta har da masu sauraro sauƙi da farin ciki mai gusar da ɓacin rai da ƙuncin tunani. 

Kasancewar duniya ta wayi gari cikin ruɗani tun daga farko-farkon shekara da ta gabata ta 2020 na samun kai cikin rashin tabbas game da ciwo ko cututtukan koronabairas (Corona ɓirus) ya sanya an rufe zirga-zirga a wurare da dama a faɗin duniya, wannan kuwa ya faru ne saboda rashin tabbas game da maganin cutar wadda ta kasance tamfar wutar daji mai kisa! Bisa wannan dalili sai kowa ya sami kansa a halin kulle wuri guda. Yayin da wasu ke ɗaukan kulle a matsayin takura da hana kataɓus, abin ba haka yake ga dukkan al’umma ba. A wurin wasu kulle kan haifar da sabon tunani da isashen lokaci na yin bincike da rubuta abin da zuciya ta saƙa ko ta ƙudurce shi. A bisa irin wannan ne aka rawaitu Ahmad ɗan Taimiyya, wanda galibi ya yi rubuce-rubucensa ne a halin yana tsare, yana cewa ita kurkun nan ni’ima ce a gurinmu, sai da mafi yawan mutane ba su sani ba. 

Saboda haka ba abin mamaki ba ne idan aka sami marubuta sun baje kolin fasaharsu a irin wannan hali na tsari da Korona ta jefa kowa ciki. Tun da dai an zauna wuri guda dole rai ya yi hararo wasu zantuka, kuma zuciya ta yi saƙa ta ƙulla zaren tunani. Wannan tunani shi ne yake tabbata a matsayin waƙa idan hannu ya rubuta ko baki ya furta ko ma aka sami dukka biyun.

Wannan littafi ɗa ne na irin wancan tunanin. Kuma littafin ya na ɗauke da waƙoƙi goma sha shida, wanda marubuta mawaƙa goma sha tara suka wallafa. Mutum goma sha ɗaya daga cikin marubutan duk sun rubuta waƙoƙi guda guda ne. Khalid Imam ya rubuta waƙoƙi uku, yayin da Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA) ya rubuta waƙa biyu, guda shi kaɗai, guda kuma shi da jama’a tasa mutum takwas. Duk da waɗannan mawaƙa sun yi waƙa da salo mabanbata da ƙafiyoyi daban-daban, amma duk waƙoƙin jigonsu iri guda ne, shi ne cutar Korana. 

Wannan sharhi ya yi nazarin waƙoƙin ta hanyar duban su ta fuskar saƙo da suke ƙoƙarin isarwa da kuma ta mahangar adabi. Wannan takarda ta taƙaita duba da waƙoƙin na da dama kuma saƙon da ke cikin su na da faɗi mutuƙa. 

Bayani game da sakonnin da waƙoƙin suke ƙunshe da su

Waɗannan waƙoƙi sun bayyana abubuwa da suka shafi wannan cuta ta hanyoyi da dama. Abubuwan da suka bayyana sun haɗa da:  

Tarihin cutar: Kamar yadda rahotanni suka bayyana wannan ciwo ya fara ne a shekarar dubu da sha tara, wannan ne dalilin da ya sanya aka raɗa masa suna Kobid-19 (Coɓid-19). An bayyana hakan a waƙar Korana Cutar zamani ta Mukhtar Spikin inda yake cewa: 

A Miladiya dubu biyu sha tara, 

Ga watan sha biyu tai tattara, 

Ta bayyana har ta kangara, 

Har ake ce mata Kobid sha tara, 

Ga shi a duk duniya tai sansani. 

 (Korona Cutar Zamani, baiti na 4)

Haka nan mun ji cewa annobar ta ɓulla ne daga wata nahiyar daban ta duniya kafin ta shigo ƙasar Hausa. Duk da akwai bayanai mabanbanta, mafi yawan marubutan sun tafi a bisa abinda duniya ta tafi a kai na cewa cutar asalinta ‘yar ƙasar Sin ce, kafin daga baya ta shigo sauran sassa na duniya. Kamar yadda Murtala Uba ya bayyana a waƙarsa mai taken Waƙar Korona: 

A Chana ta fara ‘yar gadara,

Ta keta Europe a cikin tijara,

America sai da ta yo tsirara,

Ta taushe Trump, wa’azi gare mu. 

  (Waƙar Korona, baiti na 5)

Mukhatar Spikin ya yi makamanciyar wannan magana a waƙar Korana Cutar Zamani. Ya ce:

Daga Sin sai ga ta a Turai, 

Italiya, Jamus ko ina sarai, 

Ta kama masu kuɗi da faƙirai, 

Ta kashe tsofaffi da jarirai, 

Korona annobar wanga zamani.

 (Korona Cutar Zamani, baiti na 5)

Wannan nuni ne ga tarihin annobar ta inda ta fara daga wuri guda ta shigo ko’ina kuma ba ta kyale kowa ba. Har zuwa lokacin da aka wallafar littafin duniya ta gaza gano haƙiƙa game da cutar da maganinta, kamar yadda Halliru Abdullahi ya bayyana: 

Ai Koronar wanga ƙarni, 

Ta ƙure dukkan tunanin, 

Massana kan wanga fanni, 

Sun fa ce ba su gane maganin ba. 

 (Waƙar Cutar Korona – Halliru Abdullahi, baiti na 4)

Kasancewar an rasa maganinta ya sanya babu abin da duniya ta yi sama da kulle al’umma a wuri guda tare da ɗaukan matakan rigafi. 

Yanayin cutar: Mawaƙan sun bayyana yadda yanayin ciwon Korana yake ta inda mai ɗauke da alamomin cutar zai iya gane yanayin cutar wadda take kama wuya ta sanya tari da zazzaɓi mai tsanani. A waƙar Korona a Kano, Khalid Imam ya bayyana yanayin cutar kamar haka:

…… 

Zazzaɓinta yana da ƙarfi, 

Tarinta yana da naci, 

Taurin kai ta fi jaki.

    (Korona a Kano, baiti na 10)

Irin wannan magana ta zo a waƙar Korona Cutar Zamani inda mawaƙin yake cewa: 

Alamunta an ce kamar mura, 

Maƙogwaro take kamawa almira! 

Ta sa mutum tari ka ji ja’ira! 

Ta sarƙe numfashi ya ta’azzara, 

Huhu ya yi ƙunci haka ba sukuni. 

Tana sa ciwon kai da zazzaɓi, 

Jiki yai ta ciwo duk babu daɗi, 

Ta sanya kasala a jiki tai faɗi, 

Ta riƙe maƙoshi a kasa taɗi, 

Na tsawon wasu makwanni.

 (Korona Cutar Zamani, baiti na 11-12)

Wannan bayani na nuni da kasancewar wannan littafi a matsayin wata hanya ta isar da saƙo game da yadda ciwon yake ta mahangar masana lafiya. 

Faɗakarwa game da kiyaye kai daga Korona: Duk da babu takamaiman maganin ciwon Korona, masana kiwon lafiya sun bayyana hanyoyin kau-da-bara da yin kandagarki daga ciwon, saboda haka waƙoƙin wannan kundi cike suke da faɗakarwa game da yadda za a kare kai daga cutar. Misalai a kan haka shi ne baiti a waƙar Abdullahi Lamiɗo da ke cewa: 

Maganin cutar Korona, 

Babba dai shi ne a zauna, 

A gida yawo a daina, 

Ba tare da ƙyale addu’a ba.

Addu’a kam ba kamarta, 

Ba makami samfurinta, 

Tashi duk dare don ka yi ta, 

Ba a samu kamarta gun tsari ba. 

Bayan haka ɗau mataki, 

Ka sako “mask” nan a baki, 

Hannuwa ka lizimci wanki, 

Ba sai a wurin naɗar tuwo ba.

 (Waƙar Koronabairas, baiti na 5-7)

A waɗannan baitoci an bayyana zaman gida da saka takunkunmi (mask) da wankin hannu a matsayin matakai da ke kan gaba wurin samun kuɓuta daga kamuwa ko yaɗa wannan ciwo. Sai dai wani abin sha’awa shi ne yadda marubucin ya maida hankali tare da ƙarfafa matsayin addu’a wurin kare kai daga wannan annoba. 

Ba wai Abdullahi Lamiɗo, Khalid Imam da sauran marubuta ma sun yi makamanciyar wannan magana. Khalid yana cewa:

Tuba Sallar farilla, 

Mu taru mu dinga yin su, 

Waraka duka sai mu gan ta. 

Komai tsananin masifa, 

Ban da Allah zo faɗa min, 

Wane ne maganinta? 

 (Siyasa ce Korona, baiti na 25-26)

Wannan manuniya ce game da yadda al’umma ta ke ɗaukar annobar. Na farko a matsayin cuta wadda za a iya kare kai ta hanyar rigakafin likitanci. Ni biyun shi ne yadda da yawa su ka ɗauki cutar a matsayin jarrabawa wanda za a iya cinyewa ta hanyar addu’a, tuba da barin aikin saɓo za a sami kuɓuta daga ita. Wannan ya sanya A waƙarsa mai suna waƙar Korona, Murtala Uba yake ganin cutar a matsayin hanyar hukunta masu tawaye ga biyar Mahalicci, ya kuma bayyana tuba a matsayin magani ko waraka, kamar yadda yake cewa: 

Sun yi laƙwas sun gane Allah ,

Shi ke iko duk ga jumla, 

Don haka ni na bar dalala, 

Kin wa’azi faɗakar gare mu. 

Fata Jallah Gwani Ka yaye, 

Ka yo sauyi sanyo ta janye, 

Ka buɗi idonmu mu zam a waye 

Mun yi biyarKa Ilahu gun mu.

  (Waƙar Korona-Murtala Uba, baiti na 15-16)

A nan an kalli anobar a matsayin gargaɗi, ani kuma bayyana tuba a matsayin magani daga ita. Akwai waɗanda suke ganin sai an gwama biyun. Waƙoƙin sun ambata waɗannan ra’ayoyi ta hanyar kinaya (nuni) da sarari (a fili).

Siyasa da shaku game da cutar: Annobar Korona ta zo da abubuwa masu ba da mamaki. Daga ciki akwai siyasa tsakanin manyan ƙasashe musamman China da Amurka inda suke nunawa juna hannun tare da zargin sashe game da haddasa cutar. Haka akwai kuma siyasar addini, inda wasu ke ganin hatta tsare mutane a gida wata hanya ce ta hana su yin ibada. Wannan kuwa duk da ya shafi dukkan addinai; mabiya addinin musulunci (wanda galibi al’ummar da ke magana da harshen Hausa suke bi) sun nuna zargi matuƙa, musamman da yanayin ya janyo aka dakatar da yin jam’i a a juma’a da yawa daga masallatai na hana sallolin Asham da Tahajudi a watan Ramalana da kuma taƙaita masu zuwa aikin Hajji a shekarar da ta gabata. Wannan ya sanya waƙoƙin suka yi karakaina wurin bayyana waɗannan siyasu. Yayin da wasu ke kare wani ra’ayi, wasu kuma na kare kishiyarsa. Siyasa ce Korona ta Khalid Imam ta tatauna wannan al’amari sosai. Misali akan haka shi ne game da jayayyar manyan ƙasashe, tana cewa:

Ya sanya ƙasar Amurka, 

Da Chana idan ka gan su, 

Daga zambo sai harara.

Juna kullum sukan yi, 

Wannan kan zargi wancan, 

Cewa ƙwayar Korona.

 (Siyasa ce Korona, baiti na12-13)

Ba a nan kawai Khalid ya tsaya ba, ya ambaci siyasar ci da korona da aka zargi shugabanni da shi, inda yake cewa: 

An fake da batun Korona, 

Asusu kaf garinmu, 

Sun washe babu hujja. 

Guzuma dai an fake ne, 

Karsana suka so su harba, 

Gafiya aikinta sata.

 (Siyasa ce Korona, baiti na 4-5)

A nan mawaƙin ya ɗauki ra’ayin ma su cewa ana ci ne da Korona. Kiran cutar da fakewa da guzuma a harbi karsana magana ce a dunƙule wadda ta wuce siyasar tattalin shi kaɗai ta kai har ga amfani da siyasa wurin hana masu bauta-bauta! Da farko Khalid ya kira cutar da cewa wani aiki da aka karɓo don cin riba, yana cewa: 

Kwangila ce babu fashi, 

Wadda za su sayar da riba.

A wani baiti cikin waƙarsa Khalid ya yi zargin kwagilar ta kai ga siyasar sanya sakaci ga addini har ma ya faɗi matsayinsa game da rufe masallatai, ya ce:

Inda mai ja zo da hujja, 

Ba ni sake bari na Sallah, 

Sahun Sallar farilla. 

Domin tsoron Korona, 

Da mu gane duk mu buɗe, 

Masallatai na Sallah.

 (Siyasa ce Korona, baiti na23-24)

 Amma kuma cikin marubutan akwai mai kishiyar wannan ra’ayi kamar yadda Abdullahi Lamiɗo ya ambata a waƙar Koronabairas. 

Mallamai sun yo bayani, 

Bisa Hadisi da ƙur’ani, 

Da jawaban masu fannin, 

Likitoci ba da yaudara ba. 

 (Waƙar Koronabairas, baiti na 2)

In muka duba Waƙar Cutar Korona ta Halliru Abdullahi za mu ga kamar martani yake mayarwa masu irin wancan ra’ayi na an hana salla ne don kwagila. Yana cewa:

Ban da ma tsabar jahala, 

Wa ya kai su Imamu Salla? 

Wa ya kai su biya ga Allah? 

Ba a kai su kiran Ubangji ba. 

 (Waƙar Cutar Korona -Halliru Abdullahi, baiti na 20)

Wannan manuniya ce game da yadda al’umma ta rabu haka ma marubuta suka kasu; Inda baki ya karkata, nan yawu ke zuba.  

Siyasar Korona ta taɓa har siyasar cikin gida inda aka sami wasu shugabannin siyasa da magoya bayansu na musayar zance. Musamman ta yi tsami a wasu shafukan zumunta inda mutanen Kano da na Kaduna suka dinga musayar kalamai da tsokanar juna. Mai yiwuwa wannan ne dalilin da Khalid a waƙarsa ta Idi Loton Korana ya taɓo siyasar inda yake cewa:

    ………..

A Kano mun gode Allah, 

Mu Kanawa mun bi dahir, 

Gwamna ya gane hanya, 

Gaskiya ya rungume ta, 

Ya bar wancan da gadin, 

Titi bodar garinsu. 

 (Idi loton Korona, baiti na 15)

A nan akwai siyasa da ɗaukan matsayi a fili inda Khalid ke bayyana abin da gwamnatin Kano ta yi matsayin mafi dacewar mataki saɓanin na maƙociyarta ta Kaduna. 

A taƙaitawar zance idan muka duba waɗannan waƙoƙi cike suke da bayanai game da cutar, yanayinta, abinda ta haifar dayadda mutane suka bambanta game da ita. 

Duba ta fuskar Adabi

Idan mun nazarci littafin ta fuskar adabi za mu fahimci wasu al’amura da dama. Daga ciki akwai:

Tsakanin rubutacciyar waƙa da waƙar baka  

Littafin ‘Corona Blues’, littafi ne na rubutattun waƙoƙi don haka zaton mai karatu shi ne duk waƙoƙin da aka ambata waƙoƙi ne rubutattu. Yayin da galibin waƙoƙin suna ɗauke da siffofi na rubutacciyar waƙa kamar zubi da baiti da ƙafiya, wasu cikin waƙoƙin a fili yake sun sauka da kan wannan tsari. Waɗannan waƙoƙi sun fi kama da waƙar baka. Waƙoƙin Hazbiyallahu da Waƙar Korona, dukkansu wallafar Aminu Ladan Abubakar (ALA) sun fi kama da waƙar baka. Hazbiyallahu tana ɗauke da ɗango goma goma, wanda a iya sanina rubutacciyar waƙa ba ta wuce ‘yar biyar (Muhammad, 2019; Dangambo 2007). Ita kuma Waƙar Korona an rubuta ta ne a tsarin jagora, da ‘yan amshi. Ba na mamakin haka domin duk da kasancewar ALA ya fara ne a marubuci, tuni ya yi nitso ya shiga tsundum a waƙar baka, wanda har masanan fannin suna ambotonsa da mawaƙin baka.

Buɗe waƙa  

Daga cikin siffofin rubutacciyar waƙa akwai buɗewa da jigo da rufewa. Yayin da babban jigon duka waƙoƙin wannan littafi shi ne annobar Korona, sun bambanta a ƙananun jogogin da suke ɗauke da su. Kasancewar tushen rubutacciyar waƙa waƙoƙin addinin musulunci, galibinsu akan buɗe su da ambaton Allah ko addu’a da fatan samun fatahi. Za mu ga haka a wasu cikin waƙoƙin littafin kamar ‘Hazbiyallahu’ da ‘Korona a Kano’, Waƙar ‘Korona’ da ‘Korona cutar zamani’ da ‘Ciwon cikin Barewa’ da ‘Korona na da illa’. 

Sai dai wasu cikin waƙoƙin an buɗe wasu ne da ambaton Jigon waƙar kaitsaye misali a Waƙar ‘Korona siyasa ce’, Khalid Imam ya fara wannan ne da jimlarsa mai jan hankali, inda yake cewa: 

Ya ku jama’a ku duba,

Batun lamarin korona

Akwai lauje cikinsa.

     (Siyasa ce Korona, baiti na 1)

Kwatankwacin wannan shi ne a Waƙar ‘Korona mai sarauta’, Umma Aliyu Musa ta buɗe ne da yin kinaya ga cutar inda ta ce: “Ga wata aba mai yaɗo, Ba ta miya bare a sha romo.’

Da waɗannan bayanai za mu fahimci cewa waƙoƙin wannan littafi, waƙoƙi ne irin na bayan ƙarni na sha tara, wanda jigonsu ba wai kawai addini ba ne. Suna da jigo na siyasa, rayuwa da makamantansu. Don haka marubutan kan ma yi waƙar ba tare da ka fahimci sofane ko tasirin wani addini daga gare su ba. Misali saɓanin yadda galibin waƙoƙin kan yi kira da komawa ga Allah a matsayin magani, waƙar ‘korona mai sarauta’ ta ambaci sunan Allah ne kawai a wuri biyu.  

Salo

Kusan duk waƙoƙin da su ke wannan littafi an rubuta su ne da sasauƙan ko matsakaicin salo ta inda mai karatu ya na fahimtar inda aka dosa da zarar ya karanta waƙa. Wannan ba ya rasa alaƙa da jigon littafin wanda shi ne ilimtarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa dangane da Cutar Korona. Tare da haka za mu ga marubutan sun yi amfani da salo kala-kala wurin isar da saƙonsu. Zai wahala mu game duka salon da marubutan suka yi amfani da su, amma ga misalin wasu dafa ciki na salon da aka yi amfani da su wurin isar da saƙo a cikin waƙoƙi  

Kamantawa: Marubutan sun yi amfani da salon kinaya ko kamantawa a wasu wurare cikin littafin. Misalin wannan shi ne faɗin Abdulwaraƙat a ‘Ciwon cikin barewa’. 

   Makarantu, coci, gidan casu, 

Tituna sun zam ma kamar sarari.

 (Ciwon Cikin Barewa, baiti na 9

A wannan baiti an kamanta tituna da sarari, wanda ke nufin fili fetal da ba komai a cikinsa. Hakan na nuni da yadda tituna su ka kasance a lokacin Korona inda aka hana zirga-zigar ababen hawa.  

ii. Siffantawa: A wasu wuraren an yi amfani da solon siffantawa, wanda shi ma kamantawa ne sai dai babu ambaton kalmar kamanceceniya, za a kira abu ne da wani abu kaitsaye. Irin wannan salo ya zo a inda aka ce:

….

Janye wannan guguwar cuta, 

Don ƙaunar Mahmudu ɗangata,

    (Hazbiyallahu – ALA, baiti na 5)

A wannan misali an kira cutar da guguwa wanda ke nuni a bisa ƙarfinta da yadda ta hargitsa al’amura. 

iii. Jinsintawa: Akwai maisalai da yawa na jinsinta wannan annoba ta Korona. Ga wasu cikin misalan.

….……

Yin hakan kan sa ta haihu, 

Jama’a da yawa ta danne, 

Da wuƙa domin ta yanka.

  (Korona a Kano – Khalid Imam, baiti na 5)

A wannan misali akwai mutuntarwa da aka yi ga ciwo, kuma aka ba shi jinsin mace. An kira Korana da lamirin ‘ta’ a cikin wannan baiti har sau uku. 

Bayan jinsi kasancewar mace da na miji, akwai kuma jinsi na nau’in halitta kamar mutum, ko nau’in dabbobi ko aljan da makamantansu. A ‘Idi Loton Korona’, Khalid ya jinsinta shuganbanci da kamanta zancensu da na dabbar kaza ko agwagwa wanda su aka san su da kwakwazo ba mutum ba. Ya ce:  

Masu kwakwazo a titi, 

Cewa yaƙi ake yi

 (Idi Loton Korona, baiti na 6)

Kiransu da masu kwakwazo jinsintar da su ne da kaza ko agwagwa.

iɓ. Mutuntawa: An zo da salon mutuntar da cutar korona ta hanyar bata siffar ɗan Adam. Misali: 

Tana ta’adi cutar Korona 

Ta ce dangi sam kar mu gana

….……….

  (Waƙar Korona – Murtala Uba, baiti na 10)

A nan Korona ta zamto mutum mai ɓarna wadda ta ke ta’adi ga dangi. Kuma an mutunta ta ta hanya ba ta baki da ta yi magana da cewa dangi kar su gana. 

ɓ. Dabbantarwa: A wasu wurare an ba wa Korona siffar dabba. Misali:

  A Abuja har a ɓilla, 

Ta shige ciki ta yi sheƙa. 

Tai ƙwayaye ta yi ‘ya’ya, 

Ta miƙe ƙafa a fada. 

….……

   (Annobar Korana – Khalid Imam, baiti na 8) 

Yin sheƙa da ƙwayaye aiki ne na tsuntsaye daga cikin dabbobi. Cewa da aka yi Korona ta yi sheƙa na nuna ta yi gida ta kuma sake har ta saki ƙwayaye ta ƙyanƙyashe su.

ɓi. Jaddadar ƙarfafawa/Jerin Sarƙe: Yana daga cikin salon da marubuta waƙa kan yi amfani da shi wurin isar da saƙon. Irin wannan ya zo a baituka da dama. Misalai:

Ba ta kunya ba ta tsoro, 

Ba ta sabo ba sanayya. 

 (Annobar korona – Kalid Imam, baiti na 20)

Ta na tafiya a cikin dalala 

Ta na ɓarna cuta gare mu

(Waƙar Korona – Murtala Uba, baiti na 8)

A misali na farko an maimaita kalmar ba ta a ɗango na ɗaya da na biyu kamar yadda aka sake maimaitawa a misali na biyu. Haka na kalmar tana a ɗango na uku da na huɗu a cikin misali na biyu. 

ɓii. Gangara: Akwai misalan ganagara da yawa cikin waƙoƙin littafin. Ga misali guda ɗaya

  Ta make baƙi ta kar bature 

Cutar Kobid sam ba ta ware 

Coci, masallaci ta share 

Ta na ɓarna ne duk gare mu.

 (Waƙar Korona, baiti na 7)

A nan akwai gangara a ɗango na ɗaya da biyu inda bayanin ɗangon da ke biyo baya kaitsaye na da dangantaka da wanda ya gabace shi.  

Iɗ. Tasirin al’adu, karin magana, tarihi da tatsuniya: An yi amfani da tasirin al’ada wurin isar da jawabi a wasu wurare cikin waƙoƙin littafin ta inda mai karatu ko saurare zai fahimci ma’anar ta hanyar sanin abin da aka amabata. Misali an yi amfani da: 

Karin magana 

Kurciya in ta yi kuka, 

Saƙo nata ban da wawa,

   (Annobar Korona – Khalid Imam, baiti na 26)

A wannan misali an yi kwatance ne da karin maganar kukan kurciya, wanda bahaushe ke cewa jawabi ne da mai hankali ke ganewa. Wannan na nufin an isar da saƙo ta hanyar da masu tunani za su fahimta

Tarihi 

Yi duba annobar Amwas, 

Da sahabbai ta miƙa kabari. 

    (Ciwon Cikin Barewa – Abulwaraƙat Ayagi, baiti na 30) 

Annobar Amwas wata annoba ce da aka yi a lokacin Sayyadina Umaru ɗan Kaɗɗab (RA) wadda da yawa cikin sahabbai suka rasa rayuwarsu. Wannan bayani ne na tarihi wanda wanda ya sani zai kamanta yanayin guda biyu, yanayin Korona da yanayin Amwas.

Tatsuniya /ƙirƙirarren labari

….………..

Koke yau sai Kai Ubangiji, 

Wane gogaji giji-giji, 

 (Hazbiyallahu – Aminuddeen ALA, baiti na 9)

A wannan misali an yi amfani da ƙirƙirarren labari don isar da saƙo. Gogaji da Giji-giji wasu taurari ne a Labarin Iliya ɗan Mai ƙarfi wanda Muhammadu Ingawa ya rubuta. Gogaji wani ƙarƙƙarfan dodo ne; shi kuma Giji-giji wani sadaukin mutum ne wanda in ya gaisa da mutum sai ya ruguza ƙashinsa. Don haka a wannan baiti wanda ya san labarin nan da nan zai gane siffar wanda aka kai kuka gare shi, shi ne wanda ƙarfinsa ya fi na Gogaji da na Giji-giji 

Sarrafa harshe

Baƙin kalmomi: Akwai amfani da baƙin kalmomi wanda ba kasafai ake amfani da su ba, ko kuma sabbi waɗanda zamani ya zo da su. Misali a baitin:  

  Ban da aikin ‘yan gidoga, 

Maƙiya Allah da ɗaha,

   (Siyasa ce Korona – Khalid Imam, baiti na 6)

Kalmar ‘yan gidoga baƙuwar kalma ce wadda galibi ‘yan siyasa ke amfani da ita, tana nufin aikata shirme. 

A baitin ƙarshe na waƙar ‘Korona Mai Sarauta’ an yi amfani da wata baƙuwar kalma inda marubuciyar take cewa: 

   Ya Rabbi, ƙyamushe ta cikin sauƙi, 

Haƙiƙa wannan shekara ta ishe mu darasi babba

  (Korona Mai Sarauta – Umma Aliyu Musa, baiti na 17)

Kalmar ƙyamushewa ko ƙwamishewa kalma ce baƙuwa da ‘yan zamani ke amfani da ita da nufin gamawa da wani abu ko ganin ƙarshensa. A nan ana nufin Ubangiji ya tafiyar da cutar. 

ii.Hausar Sashe: An yi amfani da hausar sashe a wasu wurare kamar: 

Ai Koronar wanga ƙarni, 

Ta ƙure dukkan tunanin, 

Massana kan wanga fanni, 

Sun fa ce ba su gane maganin ba. 

 (Waƙar Cutar Korona – Halliru Abdullahi, baiti na 4)

Kalmar wanga Hausar Sakkwatanci ce, tana nufin wannan 

iii. Arron kalmomi: Mawaƙa kan aro kalma daga wani yare don isar da saƙo, misali Murtala Uba ya haɗa Hausa da turanci, ya yi Ingausa a Waƙar Korona inda yake cewa: 

Ta tsai da ƙasa ta kulle border 

Ta zam police mai ba da order 

Ta zam killer aikinta murder 

Ta zam haɗari a gun mu

(Waƙar Korona – Murtala Uba, baiti na 11)

Kalmar boder, police, order, killer da murder dukkansu turanci ne. Wani misalin wani aron shi ne na kalmomin Larabci inda ake cewa: 

La budda uba ne zai ɗauka, 

Gwaiwarsa iyalai sai nazari.

(Ciwon Cikin Barewa – Abulwaraƙat Ayagi, baiti na 19)

Kalmar la buda, kalmar larabci ce tana nufin babu makawa ko tilas ne. 

Waƙar da ta fi kowwace aron kalmomi ita ce waƙar Aliyu Birnin Kudu. A cikin baitinsa ashirin da takwas, baiti bakwai suna ɗauke da aron kalmomi, a kusan dukkan ƙafiyarsu ta ciki. Babu laifi idan muka kira irin wannan salo da Hargitsa Balli kamar yadda wasu manazarta ke kiran baitin da aro ya yawaita inda ma’anar kan ɓoye har sai mai sauraro ya san yaren da aka yi aron daga shi. Misali inda yake cewa.  

Korona ta hana dancing, 

Mutane sun daina working, 

Wasu ma sun daina smoking, 

Du’ai ga Allah Shi ne the king, 

Allah Kai ne abin yabonmu. 

    (Korona Tana Da Illa – Aliyu Idris Birnin Kudu, baiti na 3)

Da wahala wanda Hausa kawai ya sani ya fahimci ma’anar wannan baiti ba tare da an fassara masa kalmomin turancin da ƙarshen kowanne ɗango ba.  

Aruli

Wannan sharhi bai yi ƙoƙarin auna waɗannan waƙoƙi ba saboda haka na buƙatar lokaci da nazari mai ɗan zurfi. Amma dai a duk mawaƙan guda ne ya ambaci baharin da ya yi waƙarsa, ya ce:

Ok wazanin Mutadarik ne, 

Fa’alun, Fa’alun, Fa’alun, nazari.

  (Ciwon cikin barewa – Abulwaraƙat Ayagi, baiti na 46)

Lokacin da aka rubuta waƙa

Yayin da mawaƙa na baya suke amfani da ramzi wurin bayyana lokaci ko shekarar da aka rubuta waƙa na zamani ba su fiye yin hakan ba. Guda daga cikin waƙoƙin ta bayyana tarihin rubutunta kamar haka: 

Na yo Afirilu da fourty eight, 

A twenty nai wannan shi’iri.

 (Ciwon cikin barewa – Abulwaraƙat Ayagi, baiti na 44)

Ta hanyar amfani da kalmomin aro na turanci (fouty eight, twenti) da na larabci (shi’iri) an bayyana tarihin wannan rubutu, watan Afrilu na shekarar dubu biyu da ashirin. Adadin baiti kuma shi ne arba’in da huɗu. 

Kammalawa

Wannan takarda ta yi ƙoƙarin sharhin waƙoƙin Hausa na wannan littafi na ‘Corona Blues’. Wannan rubutu ya yi sharhin ne ta hanyoyi guda biyu. An yi sharhin gama gari wanda ya duba ma’anar waƙa da saƙon da take ɗauke da shi da kuma sharhi ta hanyar adabi. ƙoƙarin sharhin shi ne fito da ma’ana da matsayin waƙoƙin a taƙaice. Sharhin bai duba waƙoƙin guda-guda ba saboda gudun tsawaitawa. 

A ƙarshe muna rufe wannan sharhi da waɗannan ‘yan baituka 

Yau fa rubutu nai da sharhi,

 Kan kundin Waƙar Korona.

Khalid na mu ya tace waƙar

 Fasihin nan yaya a guna.

Sai Isma’il ɗan Balan nan

 Malam ne kuma mai gidana.

Waƙen Turanci da Hausa

 Kwai hikima Waƙen Korona.

Na ga su ALA ya yi waƙa,

 Gun waƙar baka shi gwanina.

Waƙar Khalid ta yi ƙaye,

 Ya yi siyasa kan Korona.

Waƙar Shehi malaminmu,

 ɗan Lamiɗo Amir a guna.

Halliru Abdullahi na mu,

 Sai Mukhtari ya sha yabona.

ɗa ga Muhammadu mai Spikin,

 Yai gadon hikima sanina.

Umma ɗiyar Musa cikinmu,

 Tai waƙa nan kan Korona.

Bashir Ibrahim har da Zaza,

 Wanda ya ce da akwai Korona.

Sai Bilyaminu ɗan Ayagi,

 Mai hikimar waƙa da gunna.

Ga ɗanladi yana cikin mu,

 Waƙa tai “shu’uma Korona.”

Mun ji Korona tana da illa,

 ɗan Birinin Kudu ne ya zana

Murtala ne autan cikinku,

 Mai fatan ya ji ba Korona.

Nan zan burki, gai da CITAD,

 Wadda take yaƙar Korona.

Rabbi tsare Waƙen Korona,

 Har mu biya bayan Korona.

By ukarofi