Daga NASIR S GWANGWAZO
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin kashe Naira biliyan 80 don sake ginawa da gyara madatsar ruwa ta Alau dake Jihar Borno a wani ɓangare na ƙoƙarin shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da inganta harkokin ruwa a yankin.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja, wanda shugaba Tinubu ya jagoranta.
Utsev ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Borno za ta haɗa hannu da gwamnatin tarayya domin gudanar da aikin wanda aka shirya kammala shi cikin watanni 24.
Ya kuma jaddada cewa za a kammala kashi na farko na aikin gyaran tsakanin watan Fabrairu zuwa Yuli na shekarar 2025 domin daƙile matsalar ambaliyar ruwa a jihar.
