Ƙaramar Hukumar Jibiya a jihar Katsina za ta ɗauki nauyin karatun ya’yan yan bindigan da suka tuba

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

A wani mataki na tabbatar da dawamammen tsaro a ƙaramar hukumar Jibiya za ta ɗauki nauyin ‘ya’yan ‘yan bindigan da suka ajiye makamin su tare da amincewa da zaman lafiya.

Wannan mataki da ƙaramar hukumar ta ɗauka ya biyo bayan taron jaddada yarjejeniyar zaman lafiya karo na uku da ya gudana a ɗakin taro na ƙaramar hukumar.

Taron wanda ƙungiyar cigaban yankin ta shirya ƙarƙashin jagorancin Alhaji Gide ɗahiru ya samu halartar manyan jami’an tsaro da wasu fitattun ‘yan bindigar da suka tuba. 

Shugaban ƙaramar hukumar Jibiya, Alhaji Sirajo Ado tare da mataimakinsa Aminu Aliyu sun halarci taron, sauran sun haɗa da wakilan manyan Sojoji da manyan yan bindiga da suka haɗa da Aufu Lankai da Sule Gurbi.

A jawabinsa shugaban ƙaramar hukumar Alhaji Sirajo Ado ya bayyana mahimmancin sulhun da ya gudana a yankin da ya ce ya rage rashin jituwa tare da ƙara bunƙasa fahimtar juna a tsakanin al’ummar yankin da tsarin ‘yan ta’addan.

Ya bayyana cewa ƙaramar hukumar za ta ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan tsoffin ‘yan bindigan kan ilimin addini da na zamani har na tsawon shekara shida a matsayin gudunmawa ga zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

ɗaya daga cikin manyan tsoffin ‘yan bindigan Audu Lankai ,ya yaba da shirin sulhun tare da buƙatar a cigaba da fahimtar juna da mutunta yarjejeniya da aka cimma.

Wakilin ƙungiyar cigaban al’ummar jibiya Barista Ibrahim Sabi’u Jibiya a jawabinsa ya buƙaci a ƙara zama wajen tsagaita rigingimu da komawa kan teburin sulhu a duk lokacin da matsala ta taso.

Baya ga batun sulhu, taron ya taɓo matsalolin da suka addabi yankin kamar rashin ruwan sha, makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya.

Taron ya kammala da ƙudirin gama iya na ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da ɗaukar matakan farfaɗo da yankin da tashe tashen hankula da suka daɗe suna addabar al’ummar.

By ukarofi