Daga SANI AHMAD a Abuja
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bangaren shari”a ta Nijeriya cike ta ke da cin hanci da rashawa, sannan kuma da yawa daga cikin alƙalai da masu shari’a sun ɓaci da cin hanci da rashawa.
Da yake magana a ranar Litinin a taron makon shari’a na kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA), a Bwari da ke Abuja, El-Rufai ya ce jama’a sun fidda tsammani kan fannin shari’a saboda jinkirta shari’a da yanke hukunci na son rai da alkalai ke yi.
El-Rufai wanda shima Lauya ne ya ce ɓangaren Shari’ar Nijeriya na fama da baragurbin alƙalai da suka cika cikinsu fam da cin hanci da rashawa.
Daga nan sai ya ƙara da ɗewa shari’a a Nijeriya ta masu kuɗi ne ba talaka ba, domin su ne suka amfana da shari’a.
Sannan kuma ya soki ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas. Ya ce hakan zai iya zama dalili da za a riƙa wa dokar ƙasa hawan ƙawara ba tare da an bi abinda ya dace ba.
Daga nan sai ya shawarci ƙungiyar lauyoyin da su tabbatar da suna jan kunnen lauyoyi da kuma sa ido akan alƙalai su rika yin abinda ya dace a kotunan Nijeriya.
Sannan ba za mu riƙa kira da a gudanar da zaɓukan masu kyau a ƙasar nan ba alhalin mu kuma alƙalai sune suke cukuikuye shari’un zaɓe da bin son rai a duk lokacin da shari’a irin haka ya bayyana a gabansu.
