Jam’iyyar PDP ta yi kakkausar suka kan ƙarin farashin man fetur da kamfanin NNPC yayi. Ta bayyana haka a matsayin zalunci ga ‘yan Nijeriya.
A ranar Talata, farashin man fetur ya ya tashi daga N615 zuwa N897 a kan duk lita ɗaya.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP Debo Olugunagba ya bayyana halin ko in kula da gwamnatin APC ke nunawa ga miliyoyin ƴan Nijeriya a kan irin halin matsin rayuwa da suka tsinci kansu.
Ya cigaba da cewa, duk lokacin da farashin mai ya tashi, ya na ƙara taɓarɓarewar tattalin arziki domin fetur ya shafi kusan komai na rayuwar mu.
