Ƙarshen shekara: Muna da wadataccen fetur – IPMAN ga ƴan Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƴan kasuwar fetur ta Ƙasa, IPMAN ta yi kira ga al’umma da kada su karaya wajen sayan man fetur inda ta ce tana da isasshen man fetur a gare su yayin da ƙarshen shekara ke ƙara ƙaratowa.

Sakataren Labaran ƙungiyar, Mista Ukadike Chinedu ya bayyana a ranar Lahadi, a Abuja, kamar yadda NAN ya ruwaito.

Chinedu ya yaba wa matatar Ɗangote bisa rage farashin lita zuwa Naira 899.5 wanda hakan zai rage tsadar farashin sufuri a lokacin tafiye-tafiye na bukukuwan ƙarshen shekara.

Ya ce hakan shi ne amfanin kula da farashin daga manyan ƴan kasuwa, ya na mai cewa matatun Ɗangote da na gwamnati za su taimaka wajen yin gasa tsakanin kamfanonin fetur ga farashin.

Ya kuma yi kira ga mambobin IPMAN da su yi ƙoƙarin mayar da farashinsu zuwa sabon farashin ga kwastomominsu don samun ƙarin ciniki, ya na mai cewa duk wanda farashinsa ya yi tsada, babu wanda zai saya daga gare shi.

By Babaji