Ƙasar Sin muhimmiyar abokiyar hulɗa ce da Afrika za ta iya haɗa hannu da ita wajen yaƙi da yunwa

Daga CMG HAUSA

Wani masanin tattalin arziki na ƙasar Rwanda Egide Karuranga, ya bayyana ƙasar Sin a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ƙasashen duniya da ƙasashen Afrika za ta iya hada hannu da su, wajen yaki da ƙarancin abinci a nahiyar, saboda gogewar da take da shi da tarin fasahohin aikin gona.

Masanin na ƙasar Rwanda ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron raya muhalli na Africa Green Revolution da aka kammala a Kigali, babban birnin ƙasar.

A cewarsa, Afrika na iya koyon dabarun ƙasar Sin bisa la’akari da yadda Sin ɗin ta yi nasarar yaƙi da yunwa da tamowa.

Ya kuma bayyana cewa, ƙasar Sin za ta iya zuba jari a ɓangaren samar da ruwa da noman rani, yana mai bayyana su a matsayin tubalin dake buƙatar mayar da hankali kansu fiye da komai a tsarin matakan raya tattalin arziki.

Ya ce misali, Afrika na gwagwarmaya da noman rani da samun amfanin gona, amma Sin tana da matuƙar gogewa a wannan fanni.

Haka kuma, akwai ƙirƙire-ƙirƙiren fasahohin aikin gona da tuni aka gwada, aka aiwatar tare da ganin nasararsu a ƙasar Sin, waɗanda za a iya amfani da su a nahiyar Afrika.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha