Ƙasar Sin ta sake bayyana matsayinta kan rahoton ofishin OHCHR dangane da Jihar Xinjiang

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya sake bayyana matsayin ƙasarsa, kan rahoton da ofishin babban kwamishinan Majalisar Ɗinkin Duniya mai lura da hakkokin bil’adama, ko kuma OHCHR a taƙaice ya fitar, wanda ya shafi jihar Xinjiang ta ƙasar Sin, tare da kira ga ƙasashe membobin MƊD da su ɗora laifi kan OHCHR.

Zhao Lijian ya ce, rahoton cike yake da ƙarairayi, wanda ƙasar Amurka tare da sauran wasu ƙasashen yammacin duniya suka ƙirƙiro don cimma muradunsu na siyasa, kana, ya sake shaida cewa, ofishin OHCHR ya riga ya zama mai haɗa baki da Amurka, da sauran wasu ƙasashen yamma wajen lalata ƙasashe masu tasowa.

Zhao ya ƙara da cewa, kwanan nan ne ƙasashe sama da 60, suka gabatar da sako zuwa ga ofishin OHCHR, inda suka jaddada cewa, batun jihar Xinjiang, batun cikin gidan ƙasar Sin ne zalla, don haka sun nuna matuƙar damuwa kan irin wannan rahoton da ofishin ya rubuta ba tare da samun izini daga ƙasar Sin ba.

Haka kuma ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba kusan dubu 1 na gida da na waje, sun rubuta wasiƙa ga OHCHR, inda suka nuna adawarsu kan abun da ofishin ya yi, wato gabatar da wani rahoto game da Xinjiang wanda ya jirkita gaskiya.

Zhao ya kuma nuna cewa, a matsayinsa na wani sashi na sakatariyar MƊD, ya zama dole OHCHR ya girmama ƙa’idojin tsarin mulkin majalisar, kana, bai kamata ya yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan ƙasashe membobinta ba.

Amma rahoton da OHCHR ya fitar game da Xinjiang, wanda ke ƙarƙashin makircin Amurka da sauran wasu ƙasashen yammacin duniya, ya saba wa hakan.

Mai fassara Murtala Zhang