Ƙasar Sin na adawa da matakin Amurka na keta ƙa’idojin fitar da kayayyaki

Daga CMG HAUSA

Ma’aikatar kula da cinikayya ta ƙasar Sin, ta bayyana adawa da matakin Amurka na keta matakan fitar da kayayyaki na ƙasar, domin hana fitar da ƙananan na’urorin laturoni na Semiconductor zuwa ƙasar Sin.

Kakakin ma’akatar Shu Jueting ne ta bayyana haka, yayin taron manema labarai na jiya, domin mayar da martani ga matakin da Amurka ta ɗauka a baya-bayan nan, na hana fitar da naurorin kirar Nvidia, samfuran A100 da H100 zuwa ƙasar Sin.

Ta ce irin wannan yunƙuri ya saɓa wa ƙa’idar takara cikin adalci da kuma ƙa’idojin cinikayya da tattalin arziki na duniya.

Haka kuma zai illata haƙƙoƙi da muradun kamfanonin ƙasar Sin, har ma da na kamfanonin Amurkar.

A don haka, ta ce ya kamata Amurka ta dakatar da tafka kura-kurai da take yi nan take, ta samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ga kamfanonin Sin da na sauran ƙasashen waje, ta kuma aiwatar da abubuwa da suka dace da daidaita tattalin arzikin duniya.

Mai fassara Fa’iza Mustapha