Ƙasashe da dama na sa ran haɓaka kasuwannin cinikayyar hidimomin Ƙasar Sin ta hanyar halartar bikin CIFTIS

Daga CMG HAUSA

A halin yanzu, ana gudanar da bikin cinikayyar hidimomi na ƙasa da ƙasa na shekarar 2022 wato CIFTIS a taƙaice a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin.

A bana, akwai ƙasashe da kungiyoyin ƙasa da ƙasa guda 71 da suka kafa shagunan nune-nune ko shirya taruka a wajen bikin na wannan karo.

Ciki har da ƙasashe guda 10 da suka haɗa da ƙasar Switzerland, da Burundi, da haɗaɗɗiyar daular Larabawa da sauransu, waɗanda a karo na farko, suka kafa shagunan nune-nune a yayin bikin CIFTIS da sunayen ƙasashensu.

Jami’in sashen kula da harkokin tattalin arziki na ofishin jakadancin haɗaɗɗiyar daular Larabawa dake nan ƙasar Sin, Saeed Alghfeli ya bayyana cewa, bikin CIFTIS ya kasance ɗaya daga cikin muhimman dandaloli guda uku, dake bayyana yadda ƙasar Sin take buɗe ƙofarta ga ƙetare.

Kuma a yayin bikin na wannan karo, ƙasarsa na fatan gabatar da ƙarin bayanai game da tattalin arzikinta ga masu zuba jari na ƙasar Sin.

A yayin wannan biki, a karo na farko, Italiya ta kafa wani shagon nune-nune da sunanta.

Wakilin ofishin birnin Beijing na kwamitin cinikin waje na ƙasar Italiya Gianpaolo Bruno ya bayyana fatan samun karin abokan haɗin gwiwa a yayin wannan biki.

Ƙasar Cyprus tana yankin iyaka dake tsakanin nahiyar Turai, da ta Asiya, da ma ta Afirka.

Minista mai kula da harkokin tattalin arziki da ciniki na ofishin jakadancin ƙasar Cyprus dake kasar Sin Petrou Petros ya ce, a karo na farko, ƙasarsa ta kafa shagon nune-nune a yayin bikin CIFTIS da sunanta, domin tana fatan gabatar wa ƙarin abokai na ƙasar Sin, sana’ar hidimomi da ke akwai a ƙasar Cyprus.

Cikin shekaru 10 da suka gabata, darajar hidimomin da ƙasar Sin ta shigo daga ƙetare ta zarce dallar Amurka triliyan 4.

A matsayin wani muhimmin bikin baje koli na ƙasa, bikin CIFTIS ya samar da damamaki masu ɗimbin yawa daga dukkan fannoni ga kamfanonin ƙasashen duniya, domin su shiga manyan kasuwannin ƙasar Sin.

Mai Fassarawa: Maryam Yang