‘SANADIN KENAN’ (2)

Daga FATIMA IBRAHIM GARBA DAN-BORNO

Ci gaba daga makonnjiya…

Sulaiman yana komawa gida kai tsaye ɗakin da ya ware domin Salima ya shiga. Tana zaune ta yi tagumi. Duk da ledan fitsarin da ke jikinta hakan bai hana ɗakin ɗaukan zarni ba. Gaba ɗaya ta susuce ta zama tamkar mahaukaciya. Yadda ta zura mashi idanu yasa ya haɗe rai, “Me ya sa kike yi mini irin kallon nan?”

Ta saki murmushinta da take yawan jifansa da shi a duk lokacin da tijararsa ta motsa masa.

“Na gaya maki zan ƙara aure ko?”
Ta ɗaga kai alamun “Eh.”

Ya sake cewa, “Ko kin gaji da zaman in mayar da ke ƙarƙashin gadan?”

Da sauri ta girgiza kai tana son yin kuka. Idan da abin da ta tsana ta ji ya ambata ba zai wuce ƙarƙashin sansanin da suka yi gudun Hijira ba. Wurin yana tuna mata da abubuwa masu hargitsa ƙwaƙwalwa. Hakan ya sake tunzura shi, “Ke kuwa wacce iriyar mayya ce! Haba! Ni ban taɓa ganin ‘ya macen da ke gudun asalinta ba sai ke. Na zaci kafin zuwan Alhajinmu a can kike rayuwa? Menene sabo a ciki? To zan gyara maki wani ɗaki daga tsakar gida ki koma can, kada amaryar ta kasa zama a gidan nan saboda zarni.”

Sai yanzu ta buɗe baki ta yi magana,”To. Na gode.”

Duk rashin imani irin na Sulaiman sai da jikinsa ya so ya yi sanyi, da sauri ya yi fatali da ɗan ragowan imaninsa ɗin, ya sa kai ya fice yana zubda yamu.

Kamar yadda Mus’ab ya gargaɗi kansa akan zai fita lamarin Sulaiman da matarsa hakan ce ta faru. Ya tattarasu ya watsar ya ci gaba da sabgoginsa.

Ko haɗuwa suka yi sai dai su yi wata hirar, amma ba ya yi masa maganar Salima, bare har a kai ga zancen aurensa da yake shirin ƙarowa.

Duk da acan ƙarƙashin zuciyarsa akwai wani abu mai tsananin kaifi da yake yawaita yankansa akan Salima. Duk dauriyarsa da kauda kai wannan abun ya ƙi daina tado masa zancen Salima. Ya rasa wannan wani irin tausayi ne.

Ba ya son sanarwa mahaifiyarsa abubuwan da ke faruwa a gidan abokinsa Sulaiman. Duk da bai taɓa aure ba, amma yasan girma da darajar ‘ya mace a rayuwar aure. Ba zai taɓa mance yadda a ka yi Sulaiman ya auro Salima ba, ba zai mance kaifin hankali irin na Salima ba. Mace ce da rayuwar duniyar bata gabanta bare ƙyale-ƙyalen cikinta.

Ya furzar da zazzafan huci yana jin kamar ya je ya ƙwato Salima da ƙarfi ya sadata da likitan da yasan irin wannan lalura tasu ta yoyon fitsari.

Yana zaune, gaba ɗaya yau ya kasa duba marasa lafiya ko guda. Shi kansa yana da buƙatan a duba lafiyarsa. Sulaiman ya shigo yana fara’a. Tunda Mus’ab ya yi masa kallo ɗaya ya ji baya son ya sake yi masa na biyu, don haka ya kauda kansa gefe kawai ba tare da ya iya furta komai ba.”Mus’ab kwana biyun nan kamar baka da lafiya.”

Mus’ab ya ɗan ja tsaki tare da ƙoƙarinsa na son basarwa ya ce, “Nima kwanakin nan ina jin jikina babu daɗi. Ya aikin?”

Sai da ya nemi wuri ya zauna ya ajiye katin ɗaurin auren akan teburin Mus’ab sannan ya ce, “Sai ka kwanta kaima a dubaka. Ga katin ɗaurin auren nan an kawo sai mu je mu rarrabawa abokanmu ko?” Ya ƙarashe yana washe baki.

Kamar zai furta wata magana sai kuma ya fasa tare da jinjina kai, “Allah ya sanya alkhairi. Ka je ka sami su Abdul ku raba ni bana jin daɗin da zan iya wannan aikin.”

Duk yadda Sulaiman ya so ya bashi haɗin kai abun ya faskara. Dole ya ɗebe katin ya bar masa saura ya ce, “Ka ɗauki waɗannan ka ba likitocinku. Ni na tafi.”

Mus’ab bai ce komai ba, yana kallon shi ya fice. Ya janye idanunsa daga irin kallon da ya bi shi da shi, ya kwantar da kansa yana jin wani irin tausayin Salima yana ratsa shi. Yarinya ƙarama da cutar yoyon fitsari. Ya kasa natsuwa, ta yaya Sulaiman zai ƙi kai yarinyar nan asibiti a yi mata aiki? Tayaya mai ilmi kaman Sulaiman zai ce wai ba a warkewa daga cutar yoyon fitsari? Dama akwai jahilai a cikin masu ilmi?
Wata Nas ta shigo da sauri ta ce, “Dokto akwai mara lafiyar da ke buƙatan taimakon gaggawa.”

Babu yadda zai yi da ya wuce ya tashi ya je ceton rai. Idan zai biye Sulaiman babu ko shakka shi kansa sai ya rasa abin da ake kira hankali a jikinsa.

A daddafe ya kammala aikinsa na ranar, ya lallaɓa ya koma gida.

Bayan ya yi wanka ya natsa ya zauna a falo ya zurawa tɓ idanu. Hajiya Asiya da tun kwanaki biyu take kula da ɗanta baya cikin natsuwarsa ta ƙaraso tana kallon abincinsa har ya huce bai ci ba. “Mus’ab! Kai Mus’ab!”

Idanunsa ya juya zuwa kallon inda take. Bai yi magana ba sai idanu da ya zuba mata kamar mai tunanin abin da zai ce mata. “Wani abu yana damunka ne? Lafiyarka kuwa? Kasan akwai ciwo mai horo da rashin cin abinci ko? Ko da yake ka fini sanin hakan.”

Sunkuyar da kansa ya yi ƙasa yana wani nazari, daga bisani ya ɗago ya ce, “Umma wai dama soyayya ta gaskiya sai da me lafiya a ke yin ta?” Umma ta girgiza kai ta ce,

“Idan akwai soyayya da gaske, lalura ba komai ba ce bare har ta taka matsayin wargaza tausayi. Me ya sa ka yi mini tambayar nan?” Mus’ab ya yi ajiyar zuciya.

Ya gyara zamansa sosai ta yadda yake fuskantar Hajiya sannan ya ce, “Sulaiman ne yake wulaƙanta Salima saboda tana fama da lalurar yoyon fitsari. Bansan wurin wani dokto ya kaita ba, kasancewar ita kanta Hajiyarsa ta tsaneta tsana mai tsanani.

Kin dai san yadda a ka yi auren nan. Bayan na dawo daga tafiyan nan da na yi, Sulaiman ya sameni ya ce mini tabbatar masa Salima ba zata sami lafiya ba. A yadda ya nuna mini baya so in duba lafiyar matarsa, haka zalika ya kasa kaita wani wurin a duba lafiyarta.

Umma yanzu haka Sulaiman aure zai ƙara nan da sati ɗaya. Alhaji dai ya zuba masu idanu, da shi da Hajiyarsa suke rawansu suke kuma kiɗarsu.”

Hajiya Asiya ta yi Salati tare da dafe ƙirji.”Yanzu Ina ita Salimar take?”

Mus’ab ya ƙurawa mahaifiyarsa idanu, itama kenan da bata ganta a cikin halin da take ba a yanzu. “Hmmn.. Ina ganin tana gidansa. Umma na yanke shawarar zubawa Sulaiman idanu ya yi abin da yake so. Duniya ce tana da faɗi, tana ɗauke da azuzuwa mabambanta.

Sannan ta baza rassanta. Yana da daman da zai ɗauki duk irin ajin da ya gadama. Ya ce mini Salima ba matata ba ce, hakan yasa dole na ƙara janye kaina.” Umma ta jijjiga kai sannan ta ce, “Ka ƙyale shi, kada watarana ya ce kana son matarsa shiyasa kake matsa masa.”

Gabansa ya yi wani irin faɗuwa wanda bai taɓa jin irinsa ba. “Umma so fa kika ce.”

Ta ɗaga kai alamun haka take nufi. Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *