Klopp ya yi sanadin korar koci shida a Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jurgen Klopp ya zama kocin Liverpool a 2015, wanda ya maye gurbin Brenden Rodgers.

Klopp ya ja ragamar Liverpool zuwa wasan ƙarshe a Champions League a 2018, sai ƙungiyar ta Anfield ta lashe kofin Zakarun Turai a 2019 na farko a wajensa na shida a Liverpool.

Liverpool ta kare a mataki na biyu a kakar 2018/19 a gasar Firimiyar Ingila da haɗa maki 97 – karo na uku da aka haɗa maki mai yawa a tarihin babbar gasar tamaula ta Ingila.

A kakar 2019/20 Klopp ya ci Uefa Super Cup da kofin Fifa Club World Cup na farko da Liverpool ta ɗauka, sannan ya ci firimiyar Ingila, bayan shekara 30 rabon da ƙungiyar ta lashe kofin.

Kwazon kocin ya sa ya lashe kyautar gwarzon koci a duniya a 2019 da kuma 2020.

Klopp ya ja ragamar Liverpool ta kai wasan ƙarshe a Champions League, wadda ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid a Faransa da ci 1-0.

Sai dai Liverpool ta yi ta biyu a teburin firimiyar, biye da Manchester City wadda ta lashe kofin da tazarar maki ɗaya ƙwal.

Qungiyar ta Anfield ta lashe FA Cup da Caraboa duk a kan Chelsea a wasannin ƙarshe da suka fafata.

Klopp ya ja ragamar Liverpool a kakar 2022/23 da lashe Community Shield, bayan doke Manchester City 3-1.

Sai dai Liverpool ta fara da tashi 2-2 da Fulham a gasar Firimiya, sannan ta yi 1-1 da Crystal Palace a Anfield da rashin nasara da ci 2-1 a hannun Manchester United a Old Trafford.

To sai dai Liverpool ta huce haushinta a kan Bournemouth da ci 9-0 a wasan mako na huɗu a Anfield ranar Asabar.

Wannan cin ya sa Bournemouth ta koci Scott Parker daga aikin kocin Bournemouth.

Hakan ya sa shi ne mai horar da tamaula na shida a Ingila da Klopp ya yi sanadin rasa aiki, bayan da Liverpool ta shi ƙungiyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *