Ƙasashe 25 sun haramta tallar sigari – WHO

Spread the love

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da sabon rahoto inda ta bayyana cewa ƙasashe 110 na duniya sun sanya hoto mai ban tsoro a jikin kwalin sigari don gargaɗin jama’a. Rahoton ya nuna cewa hakan ya taimaka wajen kare rayuwar mutane biliyan 6.1 daga cututtuka masu nasaba da shan taba.

Rahoton Global Tobacco Epidemic 2025 ya bayyana cewa akwai ci gaba sosai tun daga shekarar 2007 zuwa yau, inda kasashe 25 suka ɗauki matakin hana tallace-tallace da kawata taba gaba ɗaya (plain packaging).

WHO ta yi gargaɗi kan tsoma bakin kamfanonin taba a harkokin siyasa, tare da kiran ƙasashen duniya su ƙara tsananta haraji da matakan hana taba musamman ga matasa.

By ukarofi