Biyo bayan sanarwar da Amurka ta sanar ta tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra’ila, farashin ɗanyen man fetur ya ragu da fiye da kashi 3 cikin 100, yayin da kasuwannin duniya suka samu sauƙin fargaba. Kamfanonin jigilar kaya da masana’antun kere-kere sun samu sauki sosai.
Farashin danyen fetur na Brent ya koma $69.08, yayin da WTI ya koma $66.30. Wanda hakan ci gaba ne, duba da irin yadda yaƙin ya dasa hargaba a zukatan ‘yan kasuwa.
Masana sun bayyana cewa idan aka samu tabbacin zaman lafiya mai ɗorewa, tattalin arzikin duniya zai gyaru cikin sauri. Sai dai, akwai fargabar cewa idan rikici ya sake tashi, farashin fetur zai iya ƙara hauhawa.
