A yayin babban taron ƙungiyar tsaro ta NATO da ya gudana a birnin The Hague, Firaministan Netherlands, Mark Rutte, ya bayyana cewa lokaci ya yi da ƙasashen mambobi su ƙara kashe kuɗi sosai wajen kare kansu daga barazanar Rasha da rikicin Gabas ta Tsakiya.
Rutte ya buƙaci ƙasashe su kai kashi 5 cikin 100 na GDP dinsu ga harkokin tsaro, yana mai cewa, “Idan har abinda ya faru da Iran bai farfaɗo da mu ba, to mene ne zai farka mana?”
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya gargaɗi NATO cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, Rasha na iya kai hari ga wata ƙasa mamba a nan da shekaru biyar.
