Tashin hankali ya ɓarke a biranen Belfast, Derry da Ballymena bayan da wani zargi na fyaɗe ya afku tsakanin wasu matasa ‘yan Romania da wasu matan aure. Zanga-zangar da aka fara cikin lumana ta rikiɗe zuwa tarzoma mai muni, lamarin da ya janyo fargaba a hukumomi da al’umma.
Jami’an tsaro 81 sun jikkata, yayin da aka kama mutane 36. An ƙone motocin ‘yan sanda da wasu ƙadarorin gwamnati, tare da toshe hanyoyi.
Gwamnatin Burtaniya ta sha alwashin kafa kwamitin bincike, tare da buƙatar shugabannin al’umma su shiga tsakani don daƙile rikicin kafin ya ɓarke gaba ɗaya.
