Magance matsalar yawan kashe matafiya a Filato

Spread the love

Har yanzu ‘yan Nijeriya na ci gaba da alhinin kisan da aka yi wa wasu matafiya da suka tashi daga Kaduna zuwa jihar Filato domin halartar ɗaurin aure.

Hukumomi sun ce kimanin mutum 13 ne aka kashe bayan an tare motarsu ƙirar bas mallakin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fitar da wata sanarwa yana nuna takaici kan faruwar lamarin tare da umurtar jami’an tsaro su zaƙulo tare da hukunta waɗanda suka aikata hakan.

Sai dai wannan ba shi ne lokaci na farko da aka taɓa samun irin wannan kashe-kashe ba na matafiya a jihar ta Filato mai fama da rashin tsaro.

Faɗa tsakanin al’ummar yankin ta sanya akai-akai wasu ƙalibun jihar Filato na sauke fushinsu kan masu tafiya kan titin da ya ratsa ta jihar ya haɗa da jihohi masu maƙwaftaka.

Ita dai Filato jiha ce da ta daɗe tana fama da rikice-rikice mai alaƙa da ƙabilanci da addini da kuma fafutika game da filayen noma da na kiwo.

Har ta kai cewa a shekara ta 2004 tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar a lokacin da lamura suka rincaɓe, abin da ya kai ga dakatar da zaɓaɓɓen gwamnan jihar na wancan lokaci, Joshua Dariye.

A watan Agusta na shekarar 2021 an tare wasu matafiya da suka tashi daga jihar Bauchi zuwa jihar Ondo bayan halartar taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a gidan Sheikh ɗahiru Usman Bauchi, a garin Bauchi.

Bayanai sun nuna cewa a lokacin an kashe aƙalla mutum 30 daga cikinsu, tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya afku ne a lokacin da wasu mahara suka tare motocin matafiyan a yankin Rukuba da ke Jos, inda suka hau su da duka da sara, har suka kashe su, sannan wasu suka tsallake rijiya da baya.

Haka zalika, a ranar 30 ga Satumban shekarar 2018 ne rundunar sojin Nijeriya ta sanar da ɓacewar Janar Idris Alƙali (mai ritaya) a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja, sannan daga bisani rundunar sojin ta sanar da cewa ta gano gawarsa a garin Dura-Du da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.

An fara gano motarsa ne tare da wasu motoci ciki har da wata ƙirar bas a wani kududdufi da ke Lafendeg a yankin Du na ƙaramar hukumar Jos Ta Kudu, inda ake zargin ana kashe matafiya ana jefa motocinsu a ciki, domin su ɓace ba tare da samun labari ba.

Daga baya an gano gawarsa a wani rami a yankin, inda aka binne shi bayan kashe, lamarin da ya ɗaga hankali.

Babban Hafsan Sojin ƙasan Nijeriya na wancan lokacin Laftanal Janar Tukur Buratai ya ɗauki alwashin ganin an kama tare da hukunta waɗanda suka aikata kisan.

Sai dai duk da an kama wasu mutane da dama da suke da hannu a kisan, har yanzu dai batun kashe janar ɗin yana kotu.

Haka kuma, a ranar 6 ga watan Fabrailun shekarar 2022, an tare wasu matafiya da suka taso daga jihar Kano a hanyarsu ta tafiya jihar Nasarawa, inda aka kashe huɗu daga cikinsu.

Lamarin ya afku ne a yankin Bida Bidi da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa bayan wasu mahara sun tare babbar hanyar Zaria, inda suka musu kisan gilla, sannan suka ƙona motar.

Bayan waɗanda aka kashe, wasu da dama sun jikkata, inda suka yi jinya a asibitin Bingham da ke Jos.

Na kwana-kwanan ne shi na ranar Asabar 21 ga watan Yunin 2025, inda aka samu labarin kashe aƙalla ‘yan ɗaurin aure 12 – daga baya suka koma 13 – a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan uwansu, sannan kuma an jikkata wasu mutum 11 a lamarin wanda aka yi a ranar Juma’a.

Bayanai sun nuna cewa mutum 31 a cikin motar wadda ta taso daga Zaria a jihar Kaduna, ciki har da mata da ƙananan yara kuma suna tafiya ne a motar bas mallakin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Ibrahim Umar ya ce, “mun je auren ɗan uwanmu ne, sai muka ɓace hanya. Da muka tsaya domin mu yi tambaya, kawai sai suka mana ƙawanya suka fara cewa a kashe mu. Nan suka fara kashe direban, sannan suka kashe wasu, sannan suka ƙona motar. Allah ne ya tseratar da mu.”

Daga cikin waɗanda aka kashe har da mahaifin ango da sauran ‘yan uwansa da abokan arziki.

An gano cewa, da zarar an samu irin waɗannan kisan gilan da wasu ƙalibun jihar Filato ke yi a kan matafiya, hukumomi kan ɗauki alƙawarin ɗaukar mataki na hukunta masu laifi.

Amma a tsawon shekaru, babu wani abu a zahiri da ake ganin gwamnatin jihar Filato ko na tarraya na yi domin magance matsalar ko kuma ladabtar da masu laifi a ƙauyukan jihar ta Filato.

A cewar gwamnan Kaduna, babu wani dalili da mutanen da ba su ji ba su gani ba, suna kan hanya a tare su a kashe.

“Na faɗa wa gwamnan Filato cewa dole ne a ɗauki mataki domin ba za a mayar da jiha ta koma ta kashe mutane kawai ba.”

“Na faɗa wa gwamnan cewa abin da ake yi a Filato dole a bari, idan kuma ba a bari ba to laifin gwamna ne,” inji shi.

Blueprint Manhaja na kira ga Gwamnan Jihar Filato da Gwamnatin Tarayya da su ɗauki matakai na kawo ƙarshen irin waɗannan kashe-kashen, domin kuwa su na iya kawo cikas ga ƙoƙarin Shugaba Tinubu na tabbatar da tsaro a Nijeriya.

By ukarofi