Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na aayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo koma baya ga harkar ilimi a Nijeriya
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Atiku ya bayyana manufar a matsayin “zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi” inda ya ce hakan ya saɓa wa aa’idojin tsarin aasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi.
Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar ƙarfi wajen tafiyar da harkokinsa.
Ya yi allah-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa da kuma ɓata tsarin gwamnati.
Atiku ya ce, “Wannan sabon tsari na gwamnati ba zai yi tanadi ga ɗalibai masu hazaƙa ba wanda hakan ke nuna rashin mutunta hazaƙar ilimi.”
“Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen zaƙulo ɗalibai masu hazaƙa tare da tallafa musu, ba tare da la’akari da shekarunsu ba” inji Atiku.
Atiku ya buƙaci da a bar wa gwamnatocin jihohi kula da harkokin ilimi, wanda a tunaninsa zai fi dacewa da yadda ake yi a ƙasashen duniya.
