Mun ƙara kuɗin fasfo ne don haɓaka ingancinsa – NIS

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) a ranar Litinin ta ce an yi aiwatar da ƙarin kuɗin fasfo na ƙasa da ƙasa ne don ƙara masa inganci, da kuma tabbatar da samunsa cikin ƙanƙanin lokaci.

Kwanturolan hukumar NIS a Adamawa, Ibrahim Mohammed, ya bayyana haka a ranar Litinin a Yola, a wajen ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan al’ummar jihar kan ƙarin kuɗaɗen.

Mohammed ya shaida wa mahalarta taron cewa, daga ranar 1 ga watan Satumba, masu neman fasfo a Nijeriya za su biya N50,000 na littafin fasfo mai shafuka 32 wanda zai yi aiki na tsawon shekaru biyar, wanda a baya yake a kan N35,000.

Ya ce, littafin fasfo ɗin mai shafi 64 mai ɗauke da aiki na tsawon shekaru goma zai kasance N100,000, daga N70,000.

Da yake tabbatar da ra’ayin gwamnati, ya ce: “Wannan sabon fasfo ne da aka inganta tare da sabbin tsare-tsare, wanda ya yi daidai da ƙa’idojin ƙasa da aasa.

“Yana da hoton tambarin yatsa, kuma yana da wahala a yi na boginsa ko kuma a ɓata shi, saɓanin tsohon.”

Ya shawarci masu niyyar yin sabo ko sake sabunta fasfo ɗin su da su yi ta yanar gizo ko kuma su ziyarci ofisoshin NIS.

Ya kuma buƙaci malaman addini da su wayar da kan mabiyansu kan wannan lamari, ya kuma ƙara da cewa duk wanda ya nema kafin wa’adin zai biya tsohon kuɗi ne.

By ukarofi