Sanata Nwebonyi ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta binciki rabon taki a jihohi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mataimakin mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Onyekachi Nwebonyi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙaddamar da bincike kan jinkirin rabon takin da ma’aikatar noma ta bai wa jihohi.

Nwebonyi, mai wakiltar Ebonyi ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya yi wannan roƙo ne a ranar Asabar a mahaifarsa, Mbeke, Ishieke, da ke cikin ƙaramar hukumar Ebonyi.

A yayin taron ya raba sama da buhuna 2,200 na takin zamani ga manoma a faɗin gundumarsa.

ɗan majalisar ya jaddada cewa ya zama wajibi a gudanar da bincike cikin gaggawa, domin jinkirin rabon takin na kawo cikas ga manufar samar da kayan amfanin gona a kan kari ga manoma a kakar noma ta 2024.

“Majalisar dattawa za ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya binciki waɗanda suka haddasa jinkirin. Misali, a Ebonyi, takin zamani na zuwa lokacin da manoma ke girbe amfanin gonakinsu,” inji Nwebonyi.

Ya kuma jaddada muhimmancin rabon kayan abinci a kan lokaci, yana mai ba da shawarar cewa a samar da takin zamani da sauran kayan amfanin gona tsakanin Maris zuwa Satumba domin samun nasarar girbi da kuma ƙarfafa samar da abinci a faɗin ƙasar nan.

By ukarofi