Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Wale Tinubu, babban jami’in gudanarwa na Oando, ba su da wani sha’awar sayen kamfanin OVH.
Hakan dai ya biyo bayan ikirarin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi na cewa “kamfanonin ‘yan kasuwa” da ke kusa da shugaban ƙasa Bola Tinubu ne suka yi awon gaba da komai a ɓangaren man fetur.
Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, a ranar Laraba, inda ya bayyana mamakinsa kan yadda NNPC ya sanya sashen sayar da kayayyaki a ƙarƙashin kulawar OVH, kamfanin da Oando a ƙarƙashin jagorancin Wale Tinubu, ke da kashi 49 cikin ɗari”.
Atiku ya koka da yadda ƙudirinsa na mayar da kamfanin NNPC a matsayin wani kamfani da kuma ƙara bayyana gaskiyar sa ya ruguje, yana mai bayyana shi a matsayin “samun satar kamfanin da wasu ‘yan daba a kusa da shugaban kasa suka yi”.
A martaninta ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban jami’in yada labarai na kamfanoni, Olufemi Soneye, a Abuja ranar Alhamis, NNPC ta bayyana ikirarin Atiku a matsayin ƙarar ƙarya.
A cewar kamfanin mai na gwamnati, Wale Tinubu ko shugaban ƙasa ba su da wani sha’awar sayen OVH.
Da yake maido da cewa kamfani ne mai dogaro da kai da kuma samun ribar da kwararru ke tafiyar da su, waɗanda suka himmatu wajen ƙara wa al’umma kima, kamfanin na NNPC ya bayyana cewa, an ƙayyade shawarar zuba jarin da hukumar gudanarwar ta ke yi ne bisa dogaron kasuwanci da kuma amfanin ƙasa.
