
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce ya na ƙoƙarin shigo da kamfanoni masu nagarta a harkokinsu cikin gudanarwa da kula da matatun mai na Warri da ke jihar Delta da kuma na jihar Kaduna.
Kamfanin ya wallafa jawabin ne a shafinsa na X a ranar Juma’a.
Ya ce, matatar Warri da ke jihar Delta, an ƙaddamar da buɗe ta ne a shekarar 1978.
Sannan, an gina shi ne domin raba albarkatun man fetur ga shiyyoyin Kudu da kuma Kudu-maso-Yammacin Nijeriya.
Haka nan, an buɗe matatar Kaduna ne a shekarar 1980 don ya ke samar da man fetur ga al’ummar Arewa wanda daga baya aka faɗaɗa ayyukansa a 1983 don ya ke samar da ƙari akan adadin gangar da ya kamata ya ke samarwa a kowace rana.
