‘Yan sanda sun kama masu safarar makamai a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ƴan sanda sun kama mutane uku a garin Dutsinma da albarusai guda 740 suna ƙoƙarin kai wa ƴan bindiga a dajin Yunai.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya shaida wa manema labarai a lokacin da ya ke gabatar da waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Ya ce, Abubakar Mohammed Kabir daga Kaduna, da mannir Musa daga Dutsinma da kuma Aliyu Iliya daga Safana sunyi ƙokarin kai albarusan ne ga ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Harisu a dajin Yauni da ke ƙauyen Ummada a ƙaramar hukumar Safana.

ASP Sadiq ya ƙara da cewa, su waɗannan miyagun mutanen tuni suka amsa laifinsu tare da cewa sunyi safara albarusan ne daga jihar Nassarawa.

Ya ce, nan ba da jimawa ba da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da masu laifin a gaban ƙuliya.

Jami’in yaɗa labaran ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Katsina cewa za su cigaba da yaƙi da waɗannan miyagun mutane da ma ƴan ta’adda har sai sun samu nasarar kakkaɓe su.

Har’ilayau, ƴan sandan sun kama wasu riƙaƙƙun ƴan fashi da makami su uku a garin Bature a jihar.

By Babaji