
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta samar da kwamiti na musamman don warware matsalolin da ke hana ƴan kasuwan da ke samar da mai (OPTS) da ƙungiyar samar da mai, mai zaman kanta (IPPG) raba ɗanyen mai ga matatun gida ciki har da ta Ɗangote.
A yayin wani zama da ɓangarorin biyu, ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri ya ce babban Sakataren kwamitin, Ambasada Nicholas Ela zai gabatar da sakamakon bincikensu a ranar Talata.
Ministan ya ce, an warware mafi yawancin matsalolin da ake samu daga tsarin raba ɗanyen mai na hukumar tace man fetur ta NUPRC.
Ya kuma jaddada cewa, gwamnatin tarayya na cigaba da ƙoƙarin tallafa wa matatun mai na gida ta yadda za ake samar mu su da ɗanyen mai akan lokaci.
Haka nan, ya ce dukkan kamfanonin mai a Nijeriya sun amince da zartar da tsarin ɗanyen man ga matatun.
