Ƙoƙarin da Nijeriya ke yi don kauce wa sake fama da annobar korona, Ministan Lafiya

Daga UMAR M. GOMBE

Gwamnatin Tarayya ta bada haske kan wasu matakan da ta ɗauka domin tabbatar da Nijeriya ba ta yi fama da ɓarkewar annobar korona karo na uku ba.

Yayin da wasu ƙasashen duniya suka soma sake fama da bugun annobar karo karo na uku, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aikin gwaje-gwaje da take yi domin ganowa, killacewa da kuma kula da waɗanda suka kamu da cutar.

Ehanire ya bayyana haka ne a Litinin da ta gabata a Abuja yayin da kwamitin Shugaban Ƙasa kan Yaƙi da Cutar Korona ke gabatar da bayanin ayyukansa.

A matsayinsa na mamba a kwamitin PTF, ministan ya ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaƙi da korona har sai ta bayanta a Nijeriya.

Tare da cewa za a cim ma haka ne ta hanyar sake duba muhimman wurare domin daƙile yaɗuwar cutar tare kulawa da waɗands suka harbu da ita yadda ya kamata.

Ya ci gaba da cewa, Nijeriya ta samu raguwa na adadin mutanen da ke harbuwa da cutar duk da ƙoƙarin da ta ke ci gaba da yi na aikin gwaje-gwaje.

A cewar Ministan, ya zuwa Litinin da ta gabata, adadin waɗanda aka tabbatar sun harbu da cutar ya kai mutum 161,737 sannan mutum 2,030 sun mutu sakamakon cutar.