Ƙungiya ta yabi Tinubu kan shirin wayar da kai kan sauyin yanayi

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe

Wata ƙungiya mai zaman kanta da ke Gombe, Jewel Environmental Initiative (JEI), ta yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙaddamar da shirin yawon wayar da kai kan sauyin yanayi na Renewed Hope Climate Change Awareness Tour (REHCCAT), tana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin mataki na tinkarar barazanar sauyin yanayi da ke ƙara tsananta a Najeriya.

Ƙungiyar ta ce shirin zai taimaka wajen ƙara wayar da kan jama’a, ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire tare da inganta hanyoyin kare muhalli, musamman a cikin al’ummomin da sauyin yanayi ya fi shafa.

A cikin wata sanarwa da babban daraktan ƙungiyar, Ismail Bima, ya fitar, JEI ta nuna cikakken goyon baya ga shirin, inda ta ce zai ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jama’a da ƙungiyoyi wajen kare muhalli da kuma inganta rayuwar al’ummomin da ke fuskantar ƙalubalen sauyin yanayi.

Ƙungiyar ta bayyana cewa sauyin yanayi na ci gaba da haifar da barazana ga noma da rayuwar al’ummomi a sassa daban-daban na Najeriya, musamman a yankin Arewa inda rashin tabbas na ruwan sama, hamada da kuma ƙaruwar zafi ke shafar harkokin noma.

JEI ta kuma lura cewa ƙarancin ilimi da fahimta kan sauyin yanayi a yawancin karkara na hana mutane ɗaukar matakan da suka dace wajen tinkarar sauye-sauyen muhalli.

Ƙungiyar ta ce wannan shirin yawon wayar da kai zai taimaka wajen rage wannan giɓi ta hanyar ilimantar da jama’a, karfafa haɗin gwiwa da kuma samar da sabbin hanyoyi da za su taimaka wajen ƙara juriya ga sauyin yanayi.

Haka kuma, JEI ta buƙaci ma’aikatar muhalli ta tarayya da sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa shirin ya kai har matakin karkara ta hanyar haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi.

Tun da farko dai Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da wannan shirin na ƙasa a Abuja, inda ya buƙaci gwamnatocin jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki su mayar da wayar da kai kan sauyin yanayi zuwa matakai na zahiri domin ƙarfafa juriyar Najeriya ga sauyin yanayi da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa.

By ukarofi