Ƙungiyar cigaban Funtua ta nuna damuwa kan halin rashin tsaro a yankin

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman ya nuna damuwarsa a kan halin da garin Funtua ke ciki na rashin tsaro a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Katsina.

Ya ce a yan kwanakin nan ana samun yawaitar ƙwacen waya da satar shanu a cikin garin Funtua.

Kwamred Suleiman ya bayyana cewa a baya bayan nan ɓarayin shanu suka shiga wasu unguwanni inda sukai abin gaba da shanu da dama bayan sun jikkata mutane a garin na Funtua wanda haka a cewar sa abin damuwa ne.

Shugaban ƙungiyar sai ya yi kira ga jami’an tsaro da ke yankin su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.

Ya kuma yi kira ga shugaban ƙaramar hukumar Funtua da ya ƙara ƙaimi wajan tallafawa jami’an tsaro ta hanyar samar masu da kayan aiki da zai taimaka masu wajen daƙile duk wani abinda zai kawo barazana ga tsaro a yankin.

Kwamred Suleiman ya jawo hankalin al’ummar garin Funtua a kan rawar da ya kamata su taka ta hanyar bada bayanan sirri ga jami’an tsaro na maɓoyar miyagun mutane wanda haka zai taimaka wa jami’an tsaro wajan tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ya ce ƙungiyar su za ta yi duk abinda za ta iya yi wajen tallafawa masu ruwa da tsaki don magance matsalar tsaro a yankin.

By ukarofi