Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ƙungiyar Masu Haƙa da Sarrafa Ma’adinai a Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ahmad Yusuf, ta kai ziyarar girmamawa ga sabon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Ma’adinai ta Jihar Kebbi, Honarabul Buhari Abdullahi Warrah.
A jawabin da ya gabatar yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar ya bayyana aniyar mambobinsu na bai wa hukumar cikakken goyon baya tare da kiyaye dokoki da ƙa’idojin da aka shimfiɗa domin tafiyar da ayyukan ma’adinai a jihar.
Ya ce ƙungiyar na da burin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar domin tabbatar da gaskiya, tsari da kuma ci gaba mai ɗorewa a fannin.
Haka kuma ya yaba wa Gwamna Malam Nasir Idris bisa nadin da ya yi wa Honarabul Buhari Abdullahi Warrah, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa cancanta da kwarewa.
A cewarsa, ƙungiyar na da yakinin cewa sabon shugaban zai kawo sauyi mai ma’ana tare da ɗaga martabar hukumar da kuma jihar baki ɗaya.
ƙungiyar ta kuma jaddada cewa a shirye take ta yi aiki da hukumar bisa haɗin kai da fahimtar juna, domin tabbatar da cewa ana gudanar da harkokin ma’adinai cikin adalci da riƙon amana, kamar yadda gwamnatin jihar ke fata.
Da yake mayar da martani, Honarabul Buhari Abdullahi Warrah ya gode wa mambobin ƙungiyar bisa ziyarar da suka kai masa, yana mai bayyana jin daɗinsa kan yadda suka nuna shirin bada goyon baya da kuma bin dokokin da suka shafi ayyukan ma’adinai.
Ya ba su tabbacin cewa hukumar za ta yi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki cikin gaskiya da amana domin cimma manufofin da aka kafa ta a kai.
Ya ce daga cikin manufofin akwai samar da ingantaccen kudin shiga ga jihar, buɗe guraben ayyukan yi ga matasa, tabbatar da bin doka da oda a harkokin haka da sarrafa ma’adinai, da kuma bunkasa tattalin arzikin Jihar Kebbi baki ɗaya.
Shugaban ya kuma bayyana cewa ƙofar hukumar a buɗe take ga duk masu bukatar hulɗa da ita, matuƙar za a gudanar da ayyuka bisa tsarin dokokin ƙasa da na jiha, domin ɓangaren ma’adinai ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.
