
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce bai yi kuskure ba a game da wani taƙaitaccen faifan bidiyo da aka yaɗa a shafinsa na Truth Social wanda ke nuna tsohon shugaban ƙasar Barack Obama da uwargidansa Michelle Obama a matsayin birrai.
Da yake magana da yammacin Juma’a ga manema labarai a cikin jirgin Air Force One, Trump ya dage cewa bai yi kuskure ba ta hanyar yaɗa bidiyon don haka ba ya buƙatar neman gafara.
“Ban yi kuskure ba,” inji shi, inda ya bayyana cewa bai kalli faifan gaba dayansa ba kafin a yaɗa shi a shafin nasa.
Da aka tambaye shi kai tsaye ko ya yi alla-wadai da abubuwan da ke cikin bidiyon, Trump ya amsa da cewa, “Haƙiƙa na yi.”
Bidiyon, wanda aka watsa shi da yammacin ranar alhamis, ya nuna wani makirci game da na’urorin zaɓe da aka yi amfani da su a lokacin zaben 2020 kuma ya hada da hoton wariyar launin fata na Obama da matarshi.
Kuma ya kasance akan shafin Trump na tsawon kusan awanni 12 kafin aka goge shi a safiyar Juma’a, biyo bayan shan suka da tir daga jama’a a sassan ƙasar da ma duniya baki ɗaya.
