
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta amince da ƙarin alawus ɗin shekara-shekara na tufar aiki ga ma’aikatanta da ke aikin ungozomanci a cibiyoyin lafiya daga N20,000 zuwa N80,000.
Hukumar kula da lamuran albashi da kuɗaɗen shiga da sanar da haka a wata wasiƙa da jaridar PUNCH ta samo.
Sabon ƙarin alawus ɗin na nufin an ruɓanya na baya da kaso 300, wanda zai fara aiki daga watan Junairun 2026.
A wasiƙar, wadda ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta, Ekpo Nta, hukumar ta bayar da umarnin fara biyan ungozomomin da ke aiki a dukkan asibitocin gwamnati da sabon tsarin ta tsarin biyan albashi na gwamnati, IPPIS.
Hukumar ta ƙara da cewa, daga yanzu ba za a sake biyan su daga rarar kuɗaɗe ba, saidai ana so ne su riƙa samun alawus ɗin da wasu haƙƙoƙinsu kai-tsaye daga tsarin na IPPIS.
Hakan na zuwa ne wattani kaɗan da Ƙungiyar Ungozomomi ta ƙasa (NANM) ta soki tsarin biyan N20,000 a shekara a matsayin kuɗin inifom ga mambobin nata, inda ta ce hakan ya kasa kuma ba babu darajawa acikinsa.
