Gwamnan Kaduna ya ziyarci Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa bayan sako ‘yan cocin Kajuru da aka sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kwanaki kaɗan da sako ‘yan cocin Kajuru da ‘yan bindiga suka yi awon-gaba da su.

A lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayanin abin da ya ganawar tasu ta ƙunsa ba.

Saidai, Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce bayan Gwamna Uba Sani, Sanata Adams Oshiomhole na mai wakiltar Santoriyar Edo ta Arewa ma ya ziyarci Shugaban ƙasar a ranar.

A watan Junairu ne aka samu rahoton yin garkuwa da masu ibada a cocin Ƙauyen Kurmin Walin da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru waɗanda adadinsu ya kai kusan 170.

Da fari an samu rahoton cewa guda 86 daga cikinsu sun shaƙi iskar ‘yanci inda daga bisani aka sako sauran 82 bayan hoɓɓasa daga ɓangaren hukumomin tsaro ƙarƙashin jagorancin Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro da gwamnatin jihar.

Ziyarar na zuwa ne ne ƙasa da mako guda da ‘yan ta’adda suka yi wa al’umma kisan kiyashi a Ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiaman jihar Kwara tare yin garkuwa da mata da ‘yan mata.

By Babaji