
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa Birnin Ilorin na Jihar Kwara biyo bayan mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa al’umma a ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.
Rahotanni sun bayyana cewa, aƙalla mutane sama da 100 ne aka halaka a yayin faruwar al’amarin.
A yayin isa Filin jiragen sama na Tunde Idaigbon da ke birnin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq tare da Sanata Sadiq Umar da ke wakiltar Kwara ta Arewa da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarbe shi.
Ziyarar Shettima zuwa jihar nuna damuwa ne daga ɓangaren gwamnatin tarayya game da kisan kiyashin, wanda ya jefa ɗaukacin al’ummarta cikin jimami da yadda al’amarin tsaro ke ƙara zama barazana a arewacin Kwara.
Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai gana da masu ruwa da tsaki ciki har da mai garin Woro, Sarkin Kaiama da jagororin tsaro domin duba matakin ɓarnar da harin ya yi da kuma nazari akan ayyukan tsaro.
Da fari, Shugaba Bola Tinubu ya umarci a gaggauta tura bataliyar sojoji zuwa yankin da abin ya shafa domin kauce wa sake faruwar irin haka.
A ranar Talata ne wasu ‘yan ta’adda da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka shiga yankin Woro, inda suka cinna wa gidaje wuta da halaka mutane da dama, sannan suka yi awon-gaba da mata da ‘yan mata bayan raunata wasu masu yawa.
