Jagoran ƙungiyar Hamas Isma’ila Haniyeh, ya ce farmakin da sojojin Isra’ila suka ƙaddamar kan tsakiyar birnin Gaza, ka iya rusa tattaunawar neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da suke yi.
Haniyeh ya yi gargaɗin ne bayan da dakarun Isra’ila cikin tankokin yaƙinsu suka kutsa cikin tsakar birnin yankin na Gaza a ranar Litinin, inda suka bai wa dubban Falasɗinawa umarnin barin garin, bayan da suka shafe daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin ɗin su na shan ruwan bama-bamai.
Mazauna birnin na Gaza dai sun ce ruwan wutar da dakarun Isra’ila suka yi musu ta ƙasa da sama a baya bayan nan shi ne mafi muni da suka gani cikin watanni tara da aka shafe ana gwabza yaƙi a Zirin Gaza.
Bayanai daga sahihan majiyoyi sun ce, Isra’ila ta ƙaddamar da sabon farmakin neman kakkaɓe mayakan Hamas ne, a daidai lokacin da manyan Jami’an Amurka suka isa yankin na Gabas ta Tsakiya domin shiga tsakani a sabuwar tattaunawar ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar da ake fatan ta zama ta dindindin.
Ya zuwa yanzu dai babuƙarin bayani akan yawan mutanen da suka rasa rayukansu a cikin birnin na Gaza, sai dai jami’an kai ɗaukin gaggawa sun ce ko shakkaha babu, adadin na da yawa.
