Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar jajirtattun matasan jam’iyyar APC ta ƙasa, National Youths ɓanguard of APC ta sa ƙafa ta shure ɗaukacin zarge-zargen da Hon. Aminu Sani Jaji ya yi wa Ministan ƙasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya, Dr Bello Muhammed Matawalle, cewa yana kitsa zarge-zargen ayyukan cin amanar jam’iyya a kansa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa Dr Adeniyi Wale, ya bayyana zarge-zargen Hon. Jaji a matsayin “maras tushe,” yana mai cewa hakan wata hanya ce ta karkatar da hankalin jama’a daga abubuwan da yake kullawa a siyasa.
“Jaji ya jima yana gabatar da kansa a matsayin cikakken ɗan jam’iyyar APC kuma ginshiƙin haɗin kan jam’iyya, amma ayyukansa sun nuna akasin haka. A gaskiya, dabarun siyasar da yake amfani da su sun fi mayar da hankali kan kansa fiye da ci gaban jam’iyya,” inji Wale.
ƙungiyar jajirtattun matasan na APC ɓanguard ta jaddada cewa ’yan Nijeriya na buƙatar shugabanni masu gaskiya da riƙon amana, ba masu amfani da amana ta jama’a don cimma muradunsu na ƙashin kai ba. Haka kuma, ƙungiyar ta ƙalubalanci ingancin zarge-zargen Hon Jaji, tana mai cewa yana da tarihin rashin daidaito a siyasarsa.
“Kalaman da Hon. Jaji ya yi ba su da wata hujja ƙwaƙƙwara kuma hakan ya ƙara jefa shakku kan sahihancinsa da kuma basirarsa wajen yanke hukunci,” inji sanarwar.
“Shugabanci ba wai kawai riƙe muƙami ba ne, yana buƙatar ƙwazon da zai sa jama’a su aminta da kai.”
ƙungiyar ta yaba wa Minista Matawalle kan ƙoƙarinsa wajen ƙarfafa tsaro da samar da zaman lafiya a ƙasa. Ta ce shugabancinsa ya taka rawar gani wajen inganta haɗin kai da dangantakar al’umma a faɗin Nijeriya.
“Minista Matawalle na nuna ƙwazon shugabanci na gari. A ƙarƙashin kulawarsa, an samu gagarumin ci gaba wajen ƙarfafa tsaro da kyautata alaƙa tsakanin al’ummomi,” sanarwar ta bayyana.
ƙungiyar APC ɓanguard ta kuma soki salon jagorancin Jaji, tana mai cewa ba shi da hangen nesa da nauyin da ke kan shugabanni na ƙwarai.
“Wannan ɗabi’ar rashin daidaito da Hon. Aminu Sani Jaji ke nunawa ba wai kawai tana rage ƙarfin hukuncin da ya yanke ba, har ma tana rage yarda da aminci da ’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki ke da shi a kansa,” inji Wale.
ƙungiyar ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga Matawalle tare da yin kira ga mambobin jam’iyyar APC da su ci gaba da mayar da hankali kan haɗin kai da ci gaban ƙasa, tare da ƙin yarda da duk wani yunƙuri da ka iya raunana ƙarfin jam’iyya.
