A yayin ƙaddamar da cibiyar ta Sulaiman Adebola Adegunwa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana ƙudirin gwamnatin shugaba Tinubu na magance manyan giɓin da a ke samu a fannin kiwon lafiya ta hanyar haɗin gwiwa da zuba jari a cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu, kasancewar gwamnati kaɗai ba za ta iya ɗaukar nauyi ba.
Bugu da ƙari, mataimakin shugaban ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shirin zuba jari don sabunta ɓangaren kiwon lafiya,wanda ya haɗa da ƙirƙiro sama da sabbin cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 8,800 a faɗin ƙasar da kuma inganta manyan cibiyoyin da ake dasu don kula da marasa lafiyar dake fama da cutar daji da ma wasu cuttukkukan dake yaɗuwa.
