Ƙungiyar NAWOJ ta taya Kwamishinan labaran Kano, Abdullahi Waiya murnar kammala digiri na uku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sakatariyar Ƙungiyar ‘Yan Jarida Mata ta Ƙasa (NAWOJ), na taya Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yaɗa Labara da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, murnar kammala digirinsa na digirgir (PhD).

NAWOJ a wata takarda da ta fitar ta hannun Shugabanta Aishatu Ibrahim da Sakatariyarta Wasilah Ibrahim, ta ce wannan ba iya nasarar ilimi ba ce, saidai shaida ce ta ƙoƙarinsa wajen neman ilimi, jajircewa, horo da cigaba da gina kai daga ɓangarensa.

A cewarta, akwai buƙatar a yaba wa nasarorinsa musamman ganin yadda yake hidimta wa al’umma ta ilimi da jagorancinsa, tana mai cewa a tsawon shekaru ya duƙufa wajen yin tasiri da zama jigo wajen tallafa wa ‘yan jarida a Jihar Kano.

Ƙungiyar ta kuma yaba masa kan abin da ta kira da gudanarwar harkar yaɗa labarai bisa inganci da ƙoƙarin damawa da kafafen yaɗa labarai, wanda ya sanya daraja da kimarsa ta ƙaru acikin ‘yan jairda.

Haka kuma, NAWOJ ta ce wannan mataki zai taimaka wajen faɗaɗa matakin gudunmawarsa ga shugabanci na gari, sadarwar hulɗa da jama’a da kuma ci-gaban jihar Kano.

A ƙarshe, NAWOJ ta yi masa addu’ar Allah ya yi riƙo da hannunsa wajen sanya masa hikimomi, ƙara ɗaga darajarsa da kuma sanya albarka a hidimarsa ga al’umma.

By Babaji

Leave a Reply