’Yan mata huɗu sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Jigawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan mata huɗu masu shekaru tsakanin 12 zuwa 13 sun mutu bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji takwas ya kife a tafkin Dudduru, da ke ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Laraba, 23 ga Satumba, 2026, yayin da fasinjojin ke tafiya daga ƙauyen Kwadige zuwa Kasuwar Chai Chai Sabuwa. Tafkin Dudduru yana da nisan kusan kilomita uku daga ƙauyen Kwadige.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) a Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

A cewarsa, bayanan farko sun nuna cewa iska mai ƙarfi ce ka iya haddasa kifewar kwale-kwalen yayin da yake tsallaka tafkin.

Ya bayyana sunayen waɗanda suka mutu da cewa su ne Hasiya Mu’azu, mai shekaru 13; Hauwa Lawan, mai shekaru 13; Fatima Lawan, mai shekaru 12; da Dawsiyya Lawan, mai shekaru 13.

Fasinjoji huɗu sun tsira daga hatsarin bayan manoman da ke aiki a kusa da tafkin sun garzaya wurin tare da ceto su. Mazauna ƙauyukan Kwadige da Kuna su ma sun shiga aikin ceto da kwashe waɗanda abin ya shafa.

Hukumar NSCDC ta ce daga bisani an binne gawarwakin waɗanda suka mutu bisa tsarin addinin Musulunci.

Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, CC Muhammad Kabiru Ingawa, ya jajanta wa iyalan mamatan da al’ummar Kwadige bisa wannan mummunan lamari.

Ingawa ya buƙaci mutanen da ke amfani da hanyoyin ruwa wajen sufuri da su ƙara taka-tsantsan, musamman a lokacin da ake samun iska mai ƙarfi ko wasu munanan yanayin yanayi.

Ya kuma shawarci masu tuƙin kwale-kwale da fasinjoji da su kiyaye ƙa’idojin tsaron sufuri a ruwa, tare da guje wa yin tafiye-tafiye a lokacin da yanayin iska ko ruwa zai iya jefa rayukansu cikin haɗari.

By ukarofi

Leave a Reply