Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruk Hassan Bunza, ya bayyana irin abubuwan ban tsoro da ya fuskanta bayan da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace shi tare da kai shi wani sansani a cikin daji.
Alƙali nBunza ya ce, ’yan bindiga biyar ɗauke da makamai ne suka zo suka sace shi, kuma ya bi su ba tare da nuna wata turjiya ba, inda suka nufi gabas ta wata hanya da ke bayan gidaje, kafin daga bisani su tilasta masa tafiya da ƙafa ba tare da takalmi ba har na tsawon kusan kilomita 25 zuwa sansanin Dutsen Bandan. Ya ce, a lokacin da suka isa sansanin, ya tarar da waɗansu Fulani maza biyu da aka riga aka yi garkuwa da su.
Washegari, ’yan bindigar sun nuna masa hotonsa da na Shugaban ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Abdullahi tare da bayyana masa da cewa, an ba su umarnin sace mutanen biyu, amma ba su bayyana wanda ya ba da umarnin ba. Ya ce, abin da ya fi tayar masa da hankali shine, yadda suka nuna masa rahotannin jaridu game da sace shi. Sun kuma gaya masa cewa, suna sane da rahotannin da ke cewa an bayar da umarnin biyan Naira miliyan 200, domin a sake shi.
Wannan na nuna irin yadda ’yan bindigar ke samun bayanai daga kafafen yaɗa labarai da kuma kafafen sada zumunta, har ma yayin da suke tsare da waɗanda suka sace.
Justice Bunza ya ce, ’yan bindigar da ke sansanin ba su wuce 20 ba. Ya lura cewa, suna yin girki, suna bacci, kuma suna hulɗa da iyalansu a sansanin. Haka kuma suna samun bayanai daga wasu ’yan leƙen asiri da suke zaune a cikin al’ummomin da ke kewaye da su.
Duk da kasancewar su ɗauke da makamai, ’yan bindigar suna rayuwa cikin fargaba kuma a kullum suna cikin shirin ko-ta-kwana. Wani lokaci idan suna hasashen za a kawo masu samame sukan umurce shi da ya daina tari, saboda tsoron kada ya yi amfani da hakan wajen sanar da jami’an tsaro ko waɗansu mutane inda yake.
Ya ce, bayan sun karɓi Naira milliyan 50 a matsayin kuɗin fansa, mafi yawan ’yan bindigar sun bar sansanin. Sai dai mutane biyu ne kawai suka rage, domin su ci gaba da tsare shi.
Ya ce, duk tsawon zamansa a wannan sansanin, ba wani tashin hankali sai wata rana da ɗaya daga cikinsu ya bayar da shawarar a kashe shi, amma sai bayan mahawara mai tsawo ɗayan ya haƙura akan ba za su kashe shi ba. Wannan abin ba ƙaramin tayar masa da hankali ya yi ba.
Can bayan wani lokaci ya ji shiru zuwa misalin ƙarfe 5:00 na yamma ya fahimci cewa, an bar shi, shi kaɗai. Nan take ya cire ƙyallen da aka rufe fuskarsa da shi, ya tsere da ƙafa. Bayan ya yi tafiya, ya isa wani ƙauye, inda ya samu babur na haya, wanda daga nan ya kai shi garin Bunza.
Duk da irin wannan mummunan hali da ya shiga, Justice Bunza ya ce, abin da ya faru ba zai sa ya bar aikinsa ba. “Sace ni ba zai hana ni aikina ba. Na rantse da Allah, babu wani abu a duniya da zai canza halina na aiki. Wannan abin da ya faru zai ƙara mini ƙwarin gwiwa wajen ninka ƙoƙarina,” inji shi.
